in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aiwatar da manufar dakile nukiliya kan kasashen da ba su mallake su ba alamu ne na danniya in ji jakadan Sin
2019-05-16 10:09:29 cri
Jakadan kasar Sin mai lura da warware damarar makamai Li Song, ya ce aiwatar da manufar dakile fasahohin nukiliya kan kasashen da ba su mallake makaman nukiliya ba, alamu ne na mulkin danniya da nuna fin karfi.

Li Song ya bayyana hakan ne a birnin Geneva a ranar Talata, yayin taro na 2, game da dakile yaduwar makamai, inda aka tattauna batutuwa da suka shafi dakile yaduwar makaman Nukiliya, a taron da ake fatan kammalawa a ranar 28 ga watan Junin dake tafe.

Mr. Li ya kara da cewa, amfani da wannan manufa kan wasu kasashe, na iya zama wani babban jigon da zai haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a mataki na kasa da kasa.

Jami'in ya ce har yanzu wasu kasashe na tattare da tunani irin na cacar baka, a duk lokacin da suke kallon batun tsaron kasashen su. Don haka a cewar sa, aiwatar da manufofin kashin kai, da rashin tsafta a fannin takara tsakanin yankuna, da son shigewa gaba a karfin soji, na ci gaba da kara gurgunta yanayin tsaron kasa da kasa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China