Mista Xi ya ce, ko wani wayewar kai na da ma'anarta. Akwai bambancin launin fata da harsuna daban-daban tsakanin Bil Adam, sannan akwai bambancin wayewar kai, amma cikinsu babu wanda ya fi wani. Ra'ayin bai wa launin fata da wayewar kai fifiko har ya kai ga neman gyara ko mamaye sauran wayewar kai, abu ne da bai dace da halin da ake ciki a duniya ba. Mista Xi na ganin cewa, Sin na fatan hada kai da sauran kasashen Asiya don kiyaye abubuwan tarihi na wayewar kai, don mara baya ga gadon wayewar kai. (Amina Xu)