in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#WayewarKanAsiya# Xi Jinping:Kasar Sin tana son aiwatar da shirin bunkasa sha'anin yawon bude ido da sauran kasashen Asiya
2019-05-15 11:49:42 cri
A yayin bikin kaddamar da taron musayar wayewar kan Asiya da aka yi a nan Beijing a yau Laraba, game da batun yin mu'amala da koyon al'adun wayewar kai na daban daban na kasashen Asiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyinsa 4, inda ya jaddada cewa, idan ana son bunkasa wayewar kai har abada, dole ne a yi abubuwa bisa ka'idojin da kowa yake bi, da kuma kirkiro sabbin abubuwa domin maye gurbin abubuwan da suke haifar da koma baya. Sannan ya kamata a yi kokarin taka rawar tsofaffin abubuwa masu amfani ga ci gaban wayewar kai, domin kirkiro sabbin ni'imatattun wayewar kai da za su iya kasancewa cikin dogon lokaci da wurare daban daban.

Xi Jinping ya kara da cewa, hanya mafi amfani wajen sanya a kirkiro sabbin abubuwa ita ce, sani da kuma koyon al'adun wayewar kai daban daban, inda za a iya samun wayewar kai mai kyau ta sauran al'ummomi wajen wayar da kansa. Kasar Sin tana son aiwatar da shirin bunkasa sha'anin yawon bude ido a yankunan Asiya, ta yadda za a iya kara bunkasa tattalin arzikin yankunan Asiya, da kuma bayar da karin gudummawa wajen kara sada zumunta tsakanin al'ummomin Asiya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China