in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Ebola ta kashe sama da mutune 1,100 a Kongo sakamakon karancin ayyukan jin kai
2019-05-15 11:46:25 cri
Mutane 1,705 ake kyautata zaton sun kamu da cutar Ebola a jamhuriyar demokradiyyar Kongo (DRC) tun bayan barkewar cutar a watan Augastan bara, kakakin MDD ne ya bayyana hakan.

Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa mutane 1,122 ne suka mutu tun bayan barkewar cutar, wannan ya kunshi kaso biyu bisa uku na adadin mutanen da suka kamu da cutar.

Haq ya ce, bisa kididdigar da ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA) ya bayar, ya zuwa watan Yulin bana, rabin kudade kawai da ake bukata na dala miliyan 148 ne aka samu nasarar tattarawa don ayyukan yaki da cutar ta Ebola.

Haq ya kara da cewa, an samu karancin kayayyakin jin kan al'umma da aka tsara gudanarwa a DRC, inda aka samu kashi 12% daga cikin dala biliyan 1.65 da ake nema, matakin yayi matukar kawo koma baya ga ayyukan jin kai.

A cewar wani rahoton baya bayan nan da hukumar tantance ayyukan jin kai ta fitar ya nuna cewa, hare hare da yawan tashe tashen hankula tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai da rundunar sojojin tsaro a Kongo tun a watan Mayu yayi sanadiyyar raba mutane sama da 12,000 a arewacin lardin Kivu da Ituri dake gabashin DRC.

Tserewar mutane daga yankunan da Ebola ta shafa yayi sanadiyyar yaduwar cutar, rahoton yayi gargadin cewa, mutanen da suka tsere zuwa kasar Uganda ba bisa ka'ida ba, ba tare da an tantances u ba, ya kara haifar da hadarin yaduwar cutar Ebola a makwabtan kasashe. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China