in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#WayewarKanAsiya# Xi Jinping: Za a samu tabarbarewar wayewar kai idan ba a tuntubi juna ba
2019-05-15 11:45:40 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a gun taron tattauna wayewar kan Asiya da aka yi a yau, inda ya ce, ko wane abu mai rai na bukatar bunkasuwa maimakon tsayawa guri guda, balle wayewar kai. Yin koyi da tuntubar juna a fannoni daban-daban bisa daidaito da adalci hanya ce da wayewar kai za ta samu ci gaba.

Xi Jinping ya yi kira ga kasashe daban-daban da su kawar da shinge kan musanyar ra'ayoyi a fannin al'adu da kyautata tunani don koyi da juna a fannin wayewar kai. Ya ce, Sin na fatan kara yin musanyar ra'ayi da kasashen Asiya a tsakanin matasa, kungiyoyin fararen hula, yankuna da kafofin yada labarai da sauransu, da kafa wani dandalin musanyar ra'ayi tsakanin masana da kafa wani sabon tsarin hadin kai, da kuma sa kaimi ga hadin kai a fannoni daban-daban, ta yadda za a samar da sharadi mai kyau ga musayar ra'ayi da koyi da juna kan wayewar kan Asiya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China