in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#WayewarKanAsiya#Xi Jinping:Ya kamata a yi kokarin gane kyaun nau'o'in wayewar kai
2019-05-15 11:36:31 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Laraba ya bayyana cewa, nau'o'in wayewar kai sun bambanta, kuma su ne kyawun kirkire-kirkire. A hakika babu wani sabani a tsakaninsu, kuma abin da ake bukata shi ne idanun da ke iya ganin kyaunsu. Ya ce, kyawawan abubuwa na iya tuntubar juna, kamata ya yi kasashen Asiya su inganta wayewarsu, a yayin da kuma suke samar wa sauran kasashen duniya damar bunkasa tasu wayewar.

Shugaban ya kara da cewa, ayyukan adabi da wasannin kwaikwayon talabijin su ne suka fi iya bayyana kyaun wayewar kai, kuma kasar Sin na son hada kai da kasashen da abin ya shafa, don aiwatar da shirin fassara ayyukan adabi na Asiya da kuma musayar wasannin kwaikwayon talabijin da juna, ta yadda al'ummarsu za su kara fahimtar al'adun juna.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China