Xi ya nuna cewa, wayewar kan kasar Sin wani muhimmin sashe ne na wayewar kan Asiya, tun fil azal wayewar kan kasar Sin na samun ci gaba a yayin da take kokarin gada da yin kirkire-kirkire, wadda ta nuna bukatun al'ummar kasar a fannin tunani. Ya ce nuna kirki ga makwabta da sada zumunta da kasashe daban daban, manufa ce da wayewar kan kasar Sin ke bi a fannin zama tare, da samar da gajiya ga jama'a da wadatar da jama'a jagora ce ta wayewar kan kasar Sin a fannin tunanin daraja, da yin kwaskwarima, dacewar yanayin da ake ciki hali ne na wayewar kan kasar Sin a fannin tunani.
Xi ya yi imanin cewa, kasar Sin a nan gaba za ta kara bude kofa ga kasashen duniya, tare kuma da bai wa duniya gudummowa a fannin nasarorin da za ta cimma a fannin wayewar kai. (Bilkisu)