in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#WayewarKanAsiya# Ya kamata kasashen Asiya su yi kokarin mayar da burin neman zaman rayuwa mai inganci na fararen hula ya zama abin gaskiya
2019-05-15 11:27:20 cri
A yayin bikin kaddamar da taron musayar wayewar kan Asiya da aka yi a nan Beijing a yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen Asiya suna da tarihi kusan iri daya, da burin neman ci gaba iri daya, sabo da haka, ya kamata su yi kokarin mayar da burin neman zaman rayuwa mai inganci da fararen hula suke da shi ya zama abin gaskiya.

Xi Jinping yana ganin cewa, al'ummomin Asiya suna bukatar wata nahiyar Asiya inda ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun bunkasuwa tare, da kuma bude kofofinsu ga juna. Sabo da haka, Mr. Xi ya yi fatan kasashen Asiya za su girmama da kuma amince da juna, su kuma zama tare cikin lumana, ta yadda za su iya hakuri da juna da bude kofofinsu, da kuma samun daidaito wajen bunkasa tattalin arziki bai daya, ta yadda za su iya cin moriya da neman nasara tare.

Bugu da kari, yana fatan kasashen Asiya za su yi kokari tare wajen kawar da halin koma baya da al'ummomin wasu kasashen Asiya har yanzu suke ciki, domin samar wa yara zaman rayuwar dake da isashen kayayyakin masarufi. Ya kuma yi fatan kasashen Asiya za su bi ruhun bude kofofinsu ga ketare, su hade sassan hada hadar kasuwanci, su daidaita manufofi, da hade ababen more rayuwa, da bunkasa kasuwanci maras kaidi, da kuma kulla alaka tsakanin al'ummu, ta yadda za a iya kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a Asiya, har ma a duk duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China