Da yake ganawa da Jakadan Sin a Algeria; Li Lianhe, Mohamed Loukal, ya yabawa gudunmuwar da kamfanonin kasar Sin suka bayar wajen ginin manyan ayyuka a kasar.
A nasa bangaren, Jakadan na Kasar Sin da ya fara aiki a Algeria cikin watan Disamban bara, ya ce aikinsa shi ne, bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, musamman ta hanyar bunkasa zuba jari da aiwatar da ayyukan hadin gwiwa.
A watan Oktoban bara ne tsohon ministan kula da masana'antu da ma'adinai na Algeria Youcef Yousfi, ya bayyana fatan gaggauta tattaunawa kan yadda za a taimakawa kamfanonin kasar Sin zuba jari a bangarori daban-daban na kasar, wadanda suka hada da masaku da karafa da laturoni da hakar ma'adinai. (Fa'iza Mustapha)