in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasuwa baki sun nuna ra'ayinsu kan yanayin kasuwancin Sin
2019-05-14 20:16:38 cri

Yau Talata kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana huldar tattalin arziki da cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka cewa, ana iya fahimtar ingancin muhallin kasuwancin kasar daga matakan da 'yan kasuwa baki, ciki har da 'yan kasuwan Amurka suka dauka, ya kara da cewa, a cikin rahoton yanayin kasuwanci na shekarar 2019 da bankin duniya ya fitar, an bayyana cewa, yanayin kasuwancin kasar Sin ya kyautata cikin sauri, har ya ninka sau 32, rahoton binciken muhalin kasuwancin kasar Sin na shekarar 2019 da kungiyar 'yan kasuwan Amurka dake kasar Sin ta fitar shi ma ya nuna cewa, muhallin kasuwancin kasar Sin ya kyautata a bayyane, inda ya samu amincewar kaso 80 bisa dari na kamfanoni da aka zanta da su, kana kaso 62 bisa dari suna daukar kasar Sin a matsayin kasar dake sahun gaba yayin da suke zuba jari.

Jami'in yana mai cewa, kasar Sin tana maraba da kamfanonin ketare da su kara zuba jari a kasar, za kuma ta ci gaba da yin kokari domin samar musu yanayi mai inganci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China