in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Kiron Skinner kada ki katsantar da wayewar kai
2019-05-14 16:49:15 cri

Direkta mai kula da aikin tsara manufofi ta majalisar gudanarwar Amurka Madam Kiron Skinner ta yi magana mai tada hankali, inda ta yi ikirarin cewa, takaddamar dake tsakanin Sin da Amurka na kasancewa tamkar gwagwarmayar dake tsakanin wayewar kai da ra'ayoyin da suka sabawa juna. Maganarta ta girgiza al'ummar Amurka, har ma duk duniya baki daya, wasu masana na ganin cewa, maganar ta zama abin dariya, kuma ta lalata sunan "wayewar kai", kuma ta jefa bangarorin siyasa da ilmi na Amurka cikin mawuyacin hali, da rage mutuncin majalisar gudanarwar kasar Amurka gaba daya a duniya.

Kiron Skinner ta bayyana cewa, takarar dake tsakanin Sin da Amurka tana wakiltar rigingimun wayewar kai mai tsanani, lamarin da ya nuna cewa, ba ta da ilmi ko kadan kuma ba ta ji tsoron komai ba. An lura cewa, Skinner ta yi maganar nan ne bisa tushen maganar da Samuel Phillips Huntington, shehun malami wanda ke nazarin ilmin siyasa a jami'ar Harvard ya yi kan "rigingimun wayewar kai". Bayan da aka kammala yakin cacar baka, Huntington ya taba bayar da wani rahoto mai taken "Rigingimun wayewar kai?" a kan mujallar "Harkokin diplomasiyya" a shekarar 1993, inda a karo na farko ya gabatar da tunanin rigingimun wayewar kai wanda ya bai wa al'ummun kasashen duniya mamaki matuka, a shekarar 1996, an wallafa lattafinsa mai taken "Rigingimun wayewar kai da sake ginin tsarin duniya", wanda ya alamta cewa, an kafa tsarin tunanin nan.

Ra'ayin Huntington ya ja ankali sosai a duniya, saboda yana tare da ma'anar yayata ra'ayin neman yin babakere a fannin al'adu, lamarin da ya sa masana na kasashe daban daban sun yi wa ra'ayi na Huntington suka sosai. Amma duk da haka, ra'ayin da Huntington ya gabatar na "samun jayayya tsakanin al'adu daban daban" ba ya nufin ta da jayayya tsakanin al'adu. Maimakon haka yana son bayyana dalilin da ya sa ake takaddama tsakanin al'adu, kana ya yi wa kasashen yammacin duniya gargadin cewa kada su nemi gyara al'adun sauran kasashe bisa tsarin al'adun kansu. Abin da Huntington yake nema, shi ne musayar ra'ayi, da fahimtar juna, da hadin gwiwa a tsakanin al'adu daban daban, gami da wani tsarin duniya da aka kafa shi bisa tushen kasancewar al'adu daban daban maimakon kasancewar al'adun iri daya a duniya. Sai dai a na ta bangare, Kiron Skinner ta dauki wasu kalmomin da Huntington ya fada, don bayyana wani nufi na daban. Kila ta yi haka ne domin bata fahimci ra'ayin Huntington sosai ba. Ko kuma domin son zuciya kawai.

Ban da fannin nazarin ilmi, Madam Kiron Skinner ba ta san komai kan siyasar Amurka da ma dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ba. Ta ce, irin rikicin dake tsakanin Sin da Amurka kan wayewar kai da ma tunani, Amurka ba ta taba gamuwa da shi ba. Shin abin da ta fada gaskiya ne? Bayan babban tashin hankalin da ya faru a ranar 11 ga watan Satumba a Amurka, kasar ta ta da yake-yake sau biyu a shiyyar Gabas ta Tsakiya, kuma ta fitar da manufar nuna bambanci ga musulmai, amma ba ta taba ambatar ra'ayin samun jayayya a tsakanin al'adu daban daban na Huntington ba, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wannan ra'ayin bai yi daidai ba a siyasance ga Amurka, wadda kullum ta kan yayata ra'ayin da kowa ya amince da shi a duk duniya. Gwamnatin Amurka ta fahimci cewa, wasu batutuwan za a iya yi kawai, amma ba za a iya furta su ba. In ba haka ba, ba za ta iya mayar da kanta a matsayin gidan fitila mai nuna hanya ga ci gaban al'adun duniya ba.

Abun da ya fi baiwa 'yan bokon Amurka mamaki shi ne, Kiron Skinner ta kuma ce, wannan shi ne karon farko da muka sami wata babbar abokiyar takara da ba ta farar fata ba, wanda ya bambanta takaddamar Sin da Amurka da zaman ja-in-ja tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet a lokacin yakin cacar baka. Wato abun da take nufi shi ne, tankiyar da aka yi tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet, tankiya ce da aka yi tsakanin fararen fata, amma takaddamar Amurka da Sin takaddama ce tsakanin fararen fata da wadanda ba na fararen fata ba. Irin wadannan kalaman nuna bambancin launin fata da Skinner ta yi sun jawo tashin hankali tsakanin 'yan siyasar kasar, har ma mutane daga bangarorin siyasa da ilimi na kasar sun fito fili daya bayan daya don nuna adawa da wannan nazarin da Skinner ta yi mai ban tsoro.

A hakika dai, maganar Skinner ta bayyana ainihin ra'ayin wasu Amurkawa, wato nufin farfado da "ra'ayin cacar-baka" da "dunkulewar al'adu" a zamanin wayewar kai. Kullum kasar Amurka na mayar da kanta a matsayin wadda ke bin wayewar kai ta yammacin duniya, amma tana ta neman ra'ayin mamaye duniya a fannin wayewar kai. Yanzu dai aka shiga karni na 21, amma tunanin Skinner da na wasu mutane ya tsaya a shekaru 40 da suka gabata, irin wannan ra'ayi baya dacewa da yanayin ci gaban zamani, domin ba zai hana bunkasuwar masu neman ci gaba ba, sai dai ya lahanta masu ra'ayin kadai. An ce, yanzu ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka na tsara wata manufa game da kasar Sin bisa ra'ayi na "yaki da wani irin wayewar kai mai bambanci sosai", irin wannan mataki zai murkushe wadanda ke daukar matakan da ba su dace da zamani ba.

Al'adu sun sha bambam a duniya, an fi kyau da samun al'adu iri iri a duniya. A shekaru fiye da 2200 da suka gabata, an samu masana dake da sabon tunanin dan Adam a duniya. A kasar Sin, akwai Lao Zi, da Confucius, da Mencius da sauransu, a sa'i daya kuma, akwai Socrates, da Plato, da Aristotle da sauran masanan ilmin falfasa na kasashe yammacin duniya a zirin Girka. A cikin shekaru fiye da dubu daya da suka gabata, al'adun kasashen gabashin duniya da na kasashen yammacin duniya da sauran al'adun dan Adam sun nuna girmamawa da yabo ga juna, wadanda suka kiyaye koyi da juna.

Babu rikici kan bambancin al'adu, idan wani yana son yin amfani da dalilin al'adu don ta da rikici, babu shakka mutane masu son raya al'adu da kiyaye zaman lafiya za su zarge shi. (Amina, Jamilla, Bello, Kande, Murtala, Bilkisu, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China