in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu gagarumar bunkasar cinikin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta
2019-05-14 10:49:36 cri
Kasuwar motoci masu amfani da sabon makamashi ta kasar Sin, ta samu ci gaba sosai tsakanin watannin Janairu da Afrilu, yayin da bangaren ke tsaka da fadada a hankali.

Kididdigar da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar a jiya, ta ce kimanin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta 360,000 aka sayar a cikin watanni 4 na farkon bana, adadin da ya karu da kaso 59.8 bisa dari a kan na makamancin lokaci na bara. Haka kuma, aikin kera motocin ma ya karu da kaso 58.5 bisa dari.

Bunkasar bangaren ya biyo bayan namijin kokarin da gwamnati ta yi na bunkasa kasuwarsa ta hanyar bada ragi da rangwamen haraji a kan sayen motocin domin rage gurbatar yanayi da inganta amfani da motoci masu amfani da makamshi mai tsafta. (Fa'izaMustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China