in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar 2015 idan batun ya koma gaban kwamitin sulhun MDD
2019-05-14 10:48:21 cri
Wani jami'in kasar Iran ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar za ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Iran tana da matakai daban daban da za ta dauka, ciki har da batun ficewa daga yarjejeniyar da aka cimma, idan har an mayar da batun yarjejeniyar nukiliyar gaban kwamitin sulhun MDD, Behrouz Kamalvandi, kakakin hukumar sanya ido kan shirin makaman nukiliyar Iran, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Press TV.

Matakin da Tehran din za ta dauka na yin watsi da wasu daga cikin yarjejeniyoyin nukiliyar a cewarta hakan zai bada dama ga kasashen Turai karin lokaci wajen mutunta hakkokin dake wuyansu, kana hakan zai taimakawa yarjejeniyar ta kasa da kasa komawa aihin kan turbar da ta dace, in ji Kamalvandi.

Babbar manufar yarjejeniyar nukiliyar ta JCPOA shi ne, domin samun nasarar janye takunkumin da aka kakabawa kasar Iran domin baiwa kasar damar cin gajiya daga yarjejeniyar, in ji shi.

To sai dai kuma, har yanzu akwai matakai tsaurara duk da cewa Tehran din tana mutunta yarjejeniyar, kakakin na Iran ya bayyana hakan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China