in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron UNESCO ya jaddada bukatar samun wadatuwar ruwan sha
2019-05-14 09:48:02 cri
An bude taro na farko, na hukumar UNESCO kan ruwa, jiya Litinin a birnin Paris, wanda ke da nufin kirkiro hanyoyin magance matsalolin dake da alaka da tsare-tsaren gwamnati ta fuskar samar da ruwa.

A cewar Darakta Janar na UNESCO Audrey Azouley, sama da mutane biliyan 2 ne ba sa samun ruwa a yanzu, tana mai cewa, nan gaba, ya zuwa shekarar 2050, adadin ka iya kai wa biliyan 3.

Shi kuwa Shugaban hukumar hadin gwiwa ta kasa da kasa mai lura da tsarin bunkasawa da hade makamashi a duniya GEIDCO, ya ce samar da tsarin hade makamashi a duniya, zai haifar da sauyi matakan raya makamashi da gaggauta raya makamashi mai tsafta, yana mai cewa ba mafita zai samar ga batun makamashi ba kadai, har ma da sabuwar hanyar warware matsalar albarkatun ruwa.

Taron ya samu halartar ministoci daga kasashe 37 da kwararru da masu bincike da wakilan kungiyoyin al'umma da bangarori masu zaman kansu da kuma hukumomin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China