in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda Xi Jinping ke kaunar iyali da kasa
2019-05-13 20:24:51 cri

Hotuna hudu da ke kan kantar ajiye littattafai ta Xi Jinping

Ana iya ganin wasu hotuna guda hudu a kan kantar ajiye littattafai ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, wadanda suka jawo hankalin jama'a matuka, wadannan hotunan suna nuna mana yadda Xi ya ji dadin rayuwa tare da iyayensa da matarsa da kuma diyyarsa.

Jin dadin rayuwa tare da iyali, shi ne burin shugaban kasa, kuma shi ne burin daukacin iyalan kasashen fadin duniya.

Har kullum shugaba Xi Jinping ya kasance mai zama abin koyi ga sauran jama'a a fannin girmama iyaye da kuma kulawa da mata da diyya. Yayin da yake aiki a lardin Zhejiang a matsayin darektan kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na lardin, Xi ya taba gayawa manema labaran da suka zo daga birnin Yan'an na lardin Shaanxi cewa, "Tun da muka yi aure shekaru sama da goma da suka gabata, na kan bugawa matata Peng Liyuan waya sau daya a ko wace rana, na saba da haka." Kana a karshen shekara wato a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, uwargidansa Peng Liyuan wadda shahararriyar zabiya ce a kasar ta kan halarci bikin wake-wake da raye-rayen da aka shirya domin murnar bikin bazara, kuma a duk lokacin da Xi Jinping wanda ya yi aiki a lardin Zhejiang ya komo gidansu dake birnin Beijing, ya saba hada Jiaozi yayin da yake kallon shirye-shiryen bikin ta telibijin, daga baya ya ci gaba da jiran ta, har sai matarsa ta koma gida, a karshe su ci Jiaozi tare.

A cikin iyali mai cike da kauna, har kullum suna begen juna, duk da cewa su kan rabu. Tun bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan su kan nuna wa al'ummun kasa da kasa hali na gari na gargajiyar kasar Sin wajen ba da muhimmanci ga iyali kan dandalin diflomasiyyar kasa da kasa, musamman ma a cikin manyan batutuwan kasar ta Sin.

Ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2001, ita ce ranar haihuwar Xi Zhongxun, mahaifin Xi Jinping, shekaru 88 da haihuwa, a wancan lokaci, iyalinsa ya shirya wata gagarumar liyafa domin nuna masa fatan alheri, amma Xi Jinping wanda ke aiki a lardin Fujian a matsayin gwamnan lardin, yana fama da aiki matuka, abin da ya sa bai halarci liyafar ba, a don haka ya yi bakin ciki ya rubuta wata wasika ga mahaifinsa, inda ya byayana cewa, "Tun da aka haife ni, ina tare da iyayena har tsawon shekaru 48, sannu a hankali fahimta da kauna ga iyayena suna kara zurfi. Hakika na koyi halaye na gari da dama daga wajen mahaifina."

A wasikar da Xi ya rubuta, ya nuna ban hakuri da girmamawa ga mahaifinsa, mun lura cewa, a cikin wasikar, Xi ya nuna yadda yake kaunar mahaifinsa matuka, kana mun ga alkawarin da ya yi cewa, zai gaji halin juyin juya halin da marigayin ya bari.

Ra'ayin Xi Jinping kan gida, aikin tarbiya a gida da ma dabi'un gida

Gida tamkar wata karamar kasa ce, yayin da dubun-dubatan gidaje ke zama wata kasa guda. Shugaba Xi Jinping wanda ya girma a cikin gidan da ke da dabi'u na gari, ko da yaushe yana kula da yadda dubun-dubatan gidajen jama'arsa ke rayuwa. Tun bayan taron wakilan Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da aka yi a shekarar 2012, Shugaba Xi ya sha ambata cewa, ya kamata a mai da hankali kan gida da aikin tarbiya a gida da ma dabi'un da suka shafi gida.

A yayin liyafar murnar bikin bazara na shekarar 2015, Xi ya furta cewa, "duk wani sauyin zamani da zaman rayuwa, dole ne mu mai da hankali kan aikin raya gida, wato mu dora muhimmanci a fannonin da suka shafi gida, da aikin tarbiya a gida, da ma dabi'un gida. Lamarin da ya sa dubun-dubatan gidajen al'ummar Sin kasancewa tamkar muhimmin tushe na bunkasar kasa, da ci gaban al'umma, da ma samun jituwar zamantakewar al'umma."

A ranar 12 ga watam Disamban shekarar 2016, Shugaba Xi ya bayyana a gaban wakilan gidaje mafiya nagarta a kasar Sin, cewar "ya kamata ko wane Basine ya tuna da dabi'u na gari da suka shafi gida, kamar ya kamata a girmama tsoffi da kula yara, a samu jituwa a tsakanin miji da mata da ma tsakanin 'yan uwa, iyaye mata su nuna wa yaransu kauna yayin da yara su kuma su rika nuna biyayya ga iyaye, a koyi ilmi da dabi'u, a nuna kwazo wajen kulawa da gida ba tare da kashe kudi babu gaira babu dalili ba, a martaba dokoki da ka'idoji a tsanake, ganin yadda suka kasance muhimmin karfi wajen ci gaban al'ummar Sin." Ban da wannan kuma Xi ya ce, "gida ba masauki ne kawai ba, wuri ne na kwantar da hankali." "Idan aka samu dabi'u na gari a gida, to za a samu jituwa da ci gaban gida, in ba haka ba, zuriyoyi za su dandana kudarsu, har ma hakan daga karshe ya kawo barna ga zamantakewar al'umma."

A yayin bikin murnar bikin bazara da aka gudanar a ranar 26 ga watan Janairu na shekarar 2017, shugaba Xi Jinping ya yi kashedi ga kowa da kowa cewa, kada a manta da iyalai duk da nisan dake tsakaninsu da juna ko saboda aikin da ake fama da shi ko gudanar da ayyuka ba rana ba dare. Maganar dake nuna cewa, yadda ake komawa gida a duba iyalai ta burge Sinawa sosai.

A ranar 3 ga watan Febrairu na shekarar 2019, shugaba Xi Jinping ya sake jaddadawa a gun bikin murnar bikin bazara cewa, idan kasa ba ta samu wadata da ci gaba ba, hakika iyalai ba za su samu zaman jin dadin rayuwa ba. Haka zalika kuma, idan al'umma ba ta ji dadin rayuwa ba, kasa baki daya ba za ta samu wadata da ci gaba ba. Ya kamata a hada aikin raya iyalai da raya kasa, kowane mutum da kowane iyali su ba da gudummawarsu ga kasarsu.

Ya kamata Sinawa su nuna so da kauna ga tsofaffi, su kaunaci iyalai, su kuma so juna. A karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, ana kokarin raya tunanin son iyalai a kasar Sin, wanda ya taimaka ga jin dadin rayuwar jama'a, da kuma raya al'ummar kasar Sin baki daya.(Masu fassara: Jamila Zhou, Kande Gao, Zainab Zhang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China