in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin A Shirye Take Don Tinkarar Takaddamar Ciniki
2019-05-13 13:44:51 cri

Bayan da kasar Amurka ta daga harajin kwastam da ake karba kan kayayyakin kasar Sin na dalar Amurka biliyan 200 da ake fitar da su zuwa kasar Amurka daga kashi 10% zuwa 25%, kasar ta kara barazanar cewa, za ta kaddamar da aikin fara karbar haraji na 25% kan sauran kayayyakin dalar Amurka biliyan 325 da kasar Sin ke fitar zuwa Amurka.

Yayin da kasar Amurka ke barazanar karbar karin haraji kan kayayyakin kasar Sin, a lokaci guda, an kawo karshen shawarwarin karo na 11 tsakanin Sin da Amurka, inda bangarorin 2 suka amince da ci gaba da tattaunawarsu. Yanzu haka kasar Amurka a wani bangare tana barazanar karbar karin haraji kan dukkan kayayyakin kasar Sin, yayin da a bangare na daban ta nuna niyyar ci gaba da tattaunawa da Sin. Hakan ya nuna dabararta ta matsawa kasar Sin lamba, don neman samun nasara a teburin shawarwari. Amma idan kasar Amurka ta yi nazari kan maganar mista Liu He, shugaban tawagar kasar Sin a shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da aikin ciniki, za ta fahimci cewa, kasar Sin na da wasu bukatu, wadanda ba za ta yi rangwame kansu ba, wato su " soke karin haraji da ake neman karba", "nuna gaskiya a fannin bayyana wasu alkaluma masu alaka da ciniki", da kuma "daidaita bayanan dake cikin yarjejeniyar da ake neman kullawa". Kasar Sin za ta tsaya kan wadannan bukatu na tushe, kome matsin lambar da take fuskanta.

Yanzu kasashen Sin da Amurka sun kwashe fiye da shekara 1 suna shawarwari don neman dakatar da takaddamar ciniki. An taba samun ci gaba a shawarwarin, kuma an taba ja da baya. Sai dai kasar Sin ta nuna hakuri sosai, kana tana kokarin halartar shawarwarin bisa cikakken sahihanci, domin tana sane da cewa, ba wanda zai samu cikakkiyar nasara a takaddamar ciniki, kuma matakin karbar karin hajari zai haifar da illoli ga kasar Sin, da kasar Amurka, gami da daukacin duniya baki daya. Amma wadansu bukatun kasar Sin na tushe, tamkar wani jan layi ne da kasar Sin ta shata, wanda ba za ta bar kasar Amurka ta taka ba.

Idan kasar Amurka ta ci gaba da neman karbar karin haraji kan kayayyakin Sin, to, tabbas ne kasar Sin za ta dauki wasu matakai don mayar mata da martani. Bayan da aka kwashe fiye da shekara daya ana takaddama da kasar Amurka, bangarorin kasar Sin sun saba da yanayin matsin lamba, sun kuma samu kwarewa wajen tinkarar manufofin kasar Amurka. Tuni dai kasar Sin ta fahimci cewa, matakin kasar Amurka na kara haraji tamkar caca ce, wadda ta sabawa ra'ayin jama'ar ta, don haka a karshe dai ba za ta yi nasara ba. Wani kamfanin ba da shawara na kasar Amurka mai suna "Trade Partnership Worldwide" ya sanar da wani rahoto a watan Fabrairun bana cewa, idan an fara karbar haraji na kashi 25% kan kayayyakin kasar Sin na dalar Amurka biliyan 250 da ake fitar da su zuwa kasar Amurka, to, hakan zai sa kasar Amurka ta rasa guraben aikin yi dubu 934 a shekara guda, gami da kara kudin da wani iyalin kasar Amurka mai mutane 4 ke kashewa a kowace shekara da dala 767. Sa'an nan idan an kara karbar haraji na 25% kan sauran kayayyakin kasar Sin na dala biliyan 325, hakan zai sa Amurka ta rasa guraben aikin yi dubu 2100 a duk shekara, gami da sanya wani iyalin kasar mai mutane 4 ya kara kashe dala 2000 a kowace shekara.

A nata bangare, kasar Sin ita ma za ta fuskanci matsin lamba, amma wannan nauyi ba zai wuce karfinta ba. Saboda a fannin tsarin tattalin arziki, yanzu kasar Sin tana dogaro kan sayen kayayyakin da jama'ar kasar suke yi maimakon fitar da kayayyaki, a kokarin samun karuwar GDPn ta. Sa'an nan a fannin ciniki, idan an dubi alkaluman da aka samu a watanni 4 na farkon bana, za a ga yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka ya ragu da kashi 4.8%, yayin da yawan kayayyakin da Sin take shigowa da su daga Amurka ya ragu da kashi 26.8%. Hakan ya nuna cewa, cikin sauki za a iya maye gurbin kayayykin da kasar Amurka ke fitarwa zuwa kasar Sin da kayayyaki na sauran kasashe, kana matakin karbar karin haraji ba zai iya daidaita matsalar rashin daidaito a fannin ciniki ba. (Marubuci: Wang Yu, ma'aikacin sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China