in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Namibia sun yi tsere domin murnar cikar shugaban kasar na farko shekaru 90
2019-05-13 10:34:08 cri

Al'ummar Namibia sun cika filin Augasto Neto makil, mai cike da tarihi da aka sanyawa sunan tsohon shugaban kasar, wanda ke birnin Windhoek, domin tsere don murnar cikar shugaban kasar na farko Sam Nujoma shekaru 90 da haihuwa.

Tseren ya kunshi na kilomita 5 da km 10 da kuma km 25 domin kowa ya samu shiga.

Yanzu Sam Nujoma ya bi sahun Shugaban kasar Zimbabwe na farko Robert Mugabe da takwaransu na Zambia Kenneth Kaunda, cikin wadanda suka kai shekaru 90 da doriya da ake damawa da su a bangaren siyasar kungiyar raya yankin kudancin Afrika.

Yadda mutane masu launinka fatan daban daban suka fito a jiyan, ya alamta rayuwar daya daga cikin masu fafutukar 'yancin Namibia, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga samar da adalci ga zamantakewar al'ummar Namibia da suka fito daga bangarori daban daban. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China