in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan fasinjojin da suka ratsa ta gada tsakanin Hong Kong da Zhuhai da Macao ya wuce dubu 40 a kowace rana
2019-05-13 10:29:20 cri

An cika rabin shekara da fara yin amfani da babbar gada dake tsakanin Hong Kong da Zhuhai da Macao tun watan Oktoba na shekarar 2018. An ce, a cikin wadannan watanni 6, yawan fasinjojin da suka ratsa ta wannan gada don yawon shakatawa a ketare ya wuce dubu 40 a kowace rana, kuma yawan lokacin da ake kashewa a kwastam da kuma na sufurin kayayyaki ya ragu kwarai da gaske, saboda ganin fasahohi da na'urorin sa ido na zamanin da ake amfani da su a wannan fanni.

Wannan gada ce da ta kasance irinta mafi girma dake ratsawa ta teku a fadin duniya. Tun lokacin da aka fara amfani da ita, cikin sauki mutane suna kaiwa da dawowa tsakanin lardin Guangdong da Hong Kong, kuma mutane suna matukar sha'awar ziyarar wannan gada. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China