in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata Amurka ta hana ayyukan kamfanin Huawei ba
2019-05-12 17:10:20 cri

Mai dakin gwaji dake kula da ilmin kafofin watsa labaru na jami'ar MIT Nicholas Negroponte ya bayar da bayani a kwanakin baya cewa, ya kamata a tsara manufofin sadarwa bisa ma'auni mai dacewa, bai kamata a sanya batun siyasa ba. Bai kamata Amurka ta hana ayyukan kamfanin Huawei na Sin ba, ya kamata a yi maraba da shi don sa kaimi ga tabbatar da tsaro da samun ci gaba kan tsarin sadarwa na kasar Amurka.

Mr Negroponte ya bayyana a cikin bayaninsa cewa, kasar Amurka ta hana kamfanonin kasarta yin amfani da na'urorin sadarwa na kasar Sin domin an ce an kawo barazana ta musamman. Amma a hakika, barazana ita ce zargin da aka yiwa kamfanin Huawei ba tare da tushe ba zai kawo cikas ga kasar Amurka da ta kara yin shawarwari mafi muhimmanci kan tinkarar hadarin sarrafa yanar gizo. Watakila lamarin zai hana kasar Amurka ta cimma burin samun fasahohin zamani da ci gaban tattalin arziki.

Mr Negroponte ya bayyana cewa, kamfanin Huawei kamfani ne na biyar da ya fi zuba jari ga fannin kirkire-kirkire a duniya, wanda bai yi kurkure ba ko kadan a tsarin yanar gizo a cikin shekaru 30 da suka gabata, kuma akwai kamfanonin sadarwa fiye da 500 a fadin duniya da suka nuna gamsuwa da yin amfani da hidimarsa, wadanda ba su samu kuskuren dake shafar na'urorin kamfanin Huawei ba.

Hakazalika, Mr Negroponte ya yi nuni da cewa, yayin da gwamnati ta hana manyan kamfanoni masu samar da kayayyaki ko hidima su shiga kasuwa, za a rage yin takara da juna, sai kamfanoni ba su bukatar kara zuba jari da yin kirkire-kirkire, idan aka yi hakan, masu kashe kudi za su kara kashe kudi da samun kayayyaki ko hidima maras inganci. Kana aikin hanawa zai kawo illa ga kananan kamfanonin kasar Amurka da tilasta musu yin watsi da sayan na'urorin kamfanin Huawei da darajarsu ta kai fiye da miliyan 100 da canja na'urorinsu. Watakila wasu kananan kamfanonin kasar Amurka za su rufe domin sake sayan na'urori. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China