in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WMO ta shirya bikin ranar girmamawa yayin bikin baje kolin lambunan shakatawa na duniya
2019-05-12 16:44:39 cri

Hukumar binciken yanayi ta duniya WMO ta shirya bikin ranar girmamawa a lokacin bikin baje kolin lambunan shakatawa na duniya dake ci gaba da gudana a Beijing.

Zhang Wenjian, mataimakin babban sakataren WMO, ya ce mafi yawan bala'un da aka fuskanta a shekarar 2018 wadanda tsakanin zafi da gurbatar muhalli suka haddasa, sun shafi mutane kusan miliyan 62 a duniya.

A yayin da dumamar yanayi da sauyin yanayi ke kara kamari, kana suke shafar yanayin zamantakewar al'umma da tattalin arziki, hukumar WMO ta dukufa wajen samar da muhimman ayyuka, da neman muhimman bayanai game da yadda duniya ke sauyawa, Zhang ya furta hakan ne a taron manema labarai a lokacin kaddamar da ranar girmamawa ta duniya.

Yankunan da ake baje kolin ba wai suna nuna yadda sauyin yanayin ke shafar yanayin zaman rayuwar al'umma ba ne, har ma sun kafa wani tsari na cibiyoyin dake samar da muhimman bayanai da alkaluma dake shafar hasashen yanayin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China