in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta watsa shiri game da wayewar kan Asiya kafin CDAC
2019-05-12 16:10:59 cri

Daga ranar Lahadi zuwa Talata kasar Sin za ta watsa wani shirin cikakken labari mai babi uku game da tarihin wayewar kan nahiyar Asiya wanda babban rukunin gidajen rediyo da talibijin kasar Sin CMG ya shirya, CMG ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

Labarin, mai take "Asiya: Hasken wayewar kai" zai nuna yadda nahiyar Asiya ta samu wayewar kanta ta hanyar bibiyar tarihinta na baya wanda ta samu tushen wayewar kai ta hanyar musaya da juna da kuma kyakkyawan koyon ilmi daga juna.

Masu kallo da sauraro za su more wajen kallon tarihin Ao Dai na kasar Vietnam, da Angkor Wat na Cambodia, sai Petra na kasar Jordan da kuma kifayen teku na Maldives, sannan kuma akwai tarihin shaharrun jaruman nahiyar Asiya wadanda suka yi aiki tukuru domin kafa tarihi a doron kasa.

Masu hada tarihin sun yi tafiye tafiye zuwa kasashe da yankunan Asiya kimanin 22, inda suka tattaro bayanai game tarihin wayewar kan Sinawa, da Indiyawa da kuma Mesopotamian da sauran batutuwan da suka shafi wayewar kai.

Za'a gudanar da babban taron tattaunawa kan wayewar kan Asiya CDAC a birnin Beijing tsakanin ranakun 15 zuwa 22 ga watan Mayu, inda za'a mayar da hankali ne kan cudanyar al'adu, da musaya da kuma yadda ake koyon ilmi daga wajen juna.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China