in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulawa Da Damuwar Da Ake Nunawa Juna, Muhimmin Abu Ne Wajen Warware Takaddamar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Amurka
2019-05-11 16:58:45 cri

An kawo karshen shawarwarin tattalin arziki da cinikayya bisa babban matsayi a tsakanin kasashen Sin da Amurka karo na 11 a jiya Juma'a a birnin Washington na kasar Amurka. Mamban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, kuma mai jagorantar shawarwarin tattalin arziki a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu na bangaren Sin, mista Liu He ya bayyana bayan shawarwarin cewa, bangarorin biyu sun yi mu'amala da hadin kai yadda ya kamata, bangaren Sin na yin takatsantsan kan shawarwarin da za a yi nan gaba. An ce, tawagogin tattalin arziki da cinikayyar bangarorin biyu za su yi ganawa a birnin Beijing, don ci gaba da mu'amala da inganta shawarwarin.

Yanzu ga karin bayanin da abokiyar aikinmu Bilkisu ta hada mana.

Da karfe 12 da minti 1 na daren ranar 9 ga wata bisa agogon Washington, wato karfe 12 da minti 1 na rana bisa agogon Beijing, kasar Amurka ta fara karawa Sin haraji da kaso 25% daga kaso 10%, kan kayayyakinta da darajarsu ta kai dala biliyan 200. A nata bangaren kuma, Sin ta bayar da sanarwa a wannan ranar da karfe 12 da minti 3 na rana cewa, dole ta dauki matakai domin mayar da martani kan batun.

Wannan ba abun mamaki ba ne. Tun daga watan Fabrairun bara har zuwa yanzu, an riga an kammala shawarwari a tsakanin bangarorin biyu har sau 11, ko da yake an samu muhimmin ci gaba, amma yin shawarwari ko yin cacar baki, sun zama ruwan dare a lokacin da ake kokarin daidaita takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka. Kafin shawarwarin na wannan zagaye, Amurka ta ce zata kara yawan haraji kan kayayyakin kasar Sin, hakan ya kawo damuwar sassa daban daban kan wannan shawarwarin. A karkashin irin matsin lamba, tawagar kasar Sin ta tsaida kudurin tafiya Amurka don yin shawarwari bisa shirin da aka yi, wannan mataki ne da kasar Sin ta dauka don nuna sahihanci kan warware matsalolin, da daukar nauyi kan moriyar jama'ar kasashen biyu da ma jama'ar duniya baki daya.

Amma, kasar Amurka ta yi zargin cewa, kasar Sin na fatan sake yin shawarwari kan wasu abubuwan dake cikin yarjejeniyar, zargin na nufin cewa, ba a samu nasara kan shawarwarin ba sakamakon kuskuren kasar Sin, wannan rashin adalci ne.

Da farko, an gudanar da shawarwarin ne domin musayar ra'ayoyi da warware matsaloli da kuma cimma ra'ayin bai daya, don haka kasancewar bambancin ra'ayoyi a tsakanin bangarorin biyu ba abin mamaki ba ne, kuma idan an samu canjawar ra'ayi kafin cimma yarjejeniyar ba wani abin mamaki ba ne. Bai kamata ba a maida irin sauyawa a yunkurin shawarwari a matsayin wani dalili na kara sanya haraji.

Na biyu, kasar Amurka ta yi zargin cewa, kasar Sin ta janye jiki kan matsayinta, ita kasa ce mai rashin amincewa. A hakika dai, har zuwa yanzu kasar Amurka ita kadai ke cewa, ko kasar Sin tana biyan bukatunta na kawar da damuwarta, amma bai taba ambatar ko ita kanta ta maida hankali kan damuwar kasar Sin ba.

Game da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka, kasar Sin tana dora muhimmanci kan wasu abubuwa, kuma ba za ta janye jiki kan wadannan abubuwa ba. Da farko, shi ne soke duk wani harajin da aka kara sanyawa, don farfadowar cinikayya a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Bisa yanayin da duniya ke ciki, kara sanya haraji zai kawo illa ga tattalin arzikin Sin da Amurka, har ma zai lahanta moriyar sauran kasashen duniya. Yanzu muryar nuna adawa da kara sanya harajin na karuwa a duk duniya, ciki har da jama'ar Amurka, don haka, ya kamata kasar Amurka ta girmama bukatun kasar Sin a fannin.

Game da sayen kayayyakin cinikayya, kasar Amurka tana bukatar kasar Sin da ta kara sayen kayayyaki daga wajen ta. Amma, kasar Sin ta habaka shigowar kayayyaki ne domin biyan bukatun jama'arta kan zaman rayuwa da muhimmancin ci gaban tattalin arziki mai inganci. Saboda haka, ya kamata kasar Sin ta sayi kayayyaki ne bisa yanayin da take ciki, kuma ya kamata ta sayi kayayyaki daga wajen kasashen duniya, wadanda ke da karfin takara, da samun karbuwa daga wajen jama'ar kasar Sin.

A cikin shekara daya da wani abu da suka wuce, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace wajen tinkarar kalubale daga waje. Nan gaba, kasar Sin zata ci gaba da neman bunkasuwar tattalin arziki mai inganci bisa shirinta, da biyan bukatun jama'arta kan kyautata zaman rayuwar jama'arta. A sa'i daya, zata nuna sahihanci kan mu'amala da kasar Amurka, don ciyar da shawarwarin gaba. (Mai fassara: ma'aikaciyar Sashen Hausa Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China