in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara kusan 900 aka kubutar daga hannun kungiyoyi masu dauke da makamai a arewa maso gabashin Najeriya: UNICEF
2019-05-11 16:48:41 cri
Kimanin kananan yara 894, ciki har da yara mata 106 aka kubutar daga matsayin dakarun kiyaye zaman lafiya na fararen hula wato (CJTF) a Maiduguri, shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, a kokarin da kungiyar ke yi na kawo karshen daukar kananan yara da yin amfani da su, asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) shi ne ya bada rahoton a ranar Juma'a.

"Duk wani yunkuri game da yara wanda ya dace da manufar kare 'yancin kananan yaran dole ne a aiwatar da shi kuma amfani dashi," inji Mohamed Fall, wakilin hukumar UNICEF a Najeriya kuma jami'in dake shugabantar kungiyar dake sanya ido don tabbatar da kare martabar kananan yara a Najeriya wato (CTFMR).

Kungiyar CJTF wata kungiyar dakarun fararen hula ce dake tallafawa jami'an tsaro wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a arewa maso gabashin Najeriya. Kuma an kafa ta ne a shekarar 2013, da nufin bada kariya ga al'ummomi daga fuskantar hare haren 'yan tada kayar baya.

Yara da matasan da aka sake a ranar Juma'a zasu amfana da shirin don samun damar komawa rayuwarsu cikin al'umma, kuma zai basu sabbin damammaki don cigaban rayuwarsu, kuma hakan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya mai dorewa a Najeriya, inda yaran zasu kasance 'yan kasa na gari.

A hare haren da ake cigaba da fuskanta na kungiyoyin masu dauke da makamai a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar, an dauki kananan yara sama da 3,500 aiki inda aka yi amfani dasu karkashin kungiyoyin masu dauke da makamai tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017. Wasu kuma an yi garkuwa da su, an gallaza musu, an yi musu fyade an kuma kashe su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China