Mohammed Adamu, babban jami'in hukumar 'yan sandan Najeriyar ya ce, wadanda aka kama ana zarginsu ne da hannu wajen aikata laifukan garkuwa da mutane da fashi da makamai a sassan Najeriyar, ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da wasu manyan jami'an 'yan sanda a Abuja.
Wata kididdiga ta nuna cewa, jami'an 'yan sandan suna samun galaba a yakin da suke da bata gari a duk fadin kasar, in ji jami'in dan sandan.