in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yabawa taimakon kasar Sin na cimma Muradin kayayyakin more rayuwa
2019-05-11 15:50:52 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take baiwa Najeriya wajen cimma burinta na samar da kayayyakin more rayuwa.

Bisa abin da ya kira "muhimmin yunkurin kyautata cigaban kayayyakin rayuwar kasarmu," shugaba Buhari ya yabawa gwamnatin kasar Sin a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban babban kamfanin shimfida layin dogo na kasar Sin (CRCC) Chen Fenjian a Abuja, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar.

Shugaban ya ce kayayyakin more rayuwa a Najeriya sun tabarbare a wasu shekaru da suka gabata, lamarin da ke shafar yanayin rayuwar al'umma kana lamarin yana haifar da hasarar rayukan al'umma sakamakon hadduran da ake samu wadanda ba'a iya kauce musu.

"Muna matukar godiya ga kasar Sin bisa namijin kokarinsu na sake gina mana kayayyakin more rayuwa, da kuma samar da taimakon kwararru ga kasarmu. Zamu bayar da dukkan hadin kai da goyon da ake bukata, domin ganin an farfado da dukkan muhimman kayayyakin more rayuwar da suka turkushe ko kuma suka tsufa," inji shugaba Buhari.

Chen, wanda ya jagoranci wata tawaga don ganawa da shugaban Najeriyar ya ce, kamfanin CRCC, ya fadada ayyukansa zuwa kasashen duniya 124. A Najeriya kadai, kamfanin ya samar da guraben ayyukan yi kimanin 18,000 a cikin kasar.

Daga cikin muhimman ayyukan da kamfanin na CRCC ke gudanarwa a kasar sun hada da aikin gina layin dogo, da yankin ciniki cikin yanci, da manyan hanyoyin mota da sauransu. An yi kiyasin za'a samar da ayyuka sama da 40,000 a nan gaba daga cikin ayyukan da kamfanin ke gudanarwa a Najeriya, in ji mista Chen.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China