in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun nahiyar Asiya a Beijing
2019-05-10 13:19:03 cri

Ana shirin kaddamar da taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun nahiyar Asiya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a ranar 15 ga watan da muke ciki, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron, gami da gabatar da jawabi. Sauran manyan kusoshin da zasu halarta sun hada da shugabanni na kasashen Cambodia, da Girka, da Singapore, da Srilanka, da dai sauransu. Dangane da taron.

Taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun nahiyar Asiya da za a kaddamar da shi a ranar 15 mai zuwa, takensa shi ne "Musayar ra'ayi da fasahohi tsakanin al'adu daban daban na nahiyar Asiya, gami da kulla wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya". A wajen taron, shugabannin kasashe daban daban da na kungiyoyin kasa da kasa za su tattauna yadda za a yi musayar al'adu gami da raba fasahohi tsakanin al'ummu daban daban.

Xu Lin, shi ne mataimakin darektan kwamitin shirya taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun nahiyar Asiya. Ya ce taron zai zama wani dandali mai kyau ga al'adu daban daban,

"Taron ya shafi nahiyar Asiya, gami da bude kofarsa ga al'adu daban daban na duk duniya. Mun gayyaci wakilai na kasashe 47 dake nahiyar Asiya, don su halarci taron, wadanda za su wakilci dukkan kasashen dake nahiyar Asiya. Cikinsu akwai sanannun masana a fannonin adabi, da fasahohin al'adu, da sinima, da tsoffin kayayyaki, da wadanda ke wakiltar malamai masu bada shawara ga gwamnati, da kafofin watsa labaru, da matasa, da dai sauran gungun mutane. Har ila yau, an gayyaci wakilan wasu kasashen dake waje da nahiyar Asiya don su halarci taron. Ta hakan, an kafa wani dandali mai kyau, inda al'adu daban daban zasu iya musayar ra'ayi, da koyon fasahohi na juna, don neman ci gaba tare."

Taron dai zai kunshi bukukuwa fiye da 110, cikin su har da baje koli na al'adun Asiya, da na abincin kasashen Asiya, da na al'adun gargajiyar da aka gada daga kaka da kakani, da na fasahohin al'adu na Asiya. Dangane da lamarin, Zhang Xu, mataimakin ministan al'adu da yawon shakatawa na kasar Sin, ya ce,

"Karkarshin tsarin taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun Asiya muna da dimbin bukukuwa masu alaka da al'adu da kuma yawon shakatawa, wadanda zasu nuna tunani mai zurfi, gami da baiwa jama'a cikakkiyar damar dandanon al'adu daban daban da kansu. Ta wadannan bukukuwa ne za a kara azama ga cudanyar al'adu tsakanin kasashen Asiya, da musayar ra'ayi tsakanin masu sana'ar yawon shakatawa na kasar Sin da na sauran kasashen nahiyar Asiya."

Yawan al'ummar nahiyar Asiya ya kai kashi 2 cikin kashi 3 na daukacin al'ummar duniya. Kana wannan nahiyar ta kunshi kabilu fiye da 1000, da kasashe 47, da al'adu iri-iri kamarsu al'adun Islama, da na Kirista, da na Indiya, da na kasar Sin, da dai sauransu. Ma iya cewa, nahiyar Asiya ita ce wani wurin da ya wakilci yadda al'adu daban daban ke kasancewa tare cikin jituwa. A cewar Xu Lin, mataimakin darektan kwamitin shirya taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun nahiyar Asiya, makasudin shirya taron shi ne domin karfafa musayar fasahohi masu ci gaba tsakanin al'adu daban daban, a cewarsa,

"Idan mun yi nazari kan tarihin dan Adam, za mu gano cewa, an fara shuka alkama a yankin tudu na Anatonia dake kasar Turkiyya na yanzu, sa'an nan shinkafa an fara samunta a yankin kogin Yangtse na kasar Sin, yayin da auduga an fara dasa ta a kasar Indiya, wadanda daga bisani suka karade wurare daban daban na duniyarmu, suka zama muhimman abubuwan da dan Adam ke dogaro a kai. Wannan wani misali ne na cudanyar al' adu, da raba fasahohi."

Xu Lin ya ce, ana fatan gudanar wannan taron za ta baiwa mutanen kasashe daban daban damar musayar al'adunsu masu kyau, da ci gaba da kokarin kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin daukacin bil Adama. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China