in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Kamaru ta ce a shirye take ta tattauna da 'yan aware
2019-05-10 11:06:30 cri
Firaiministan jamhuriyar Kamaru Joseph Dion Ngute yace gwamnatinsa a shirye take ta tattauna da bangaren 'yan awaren kasar masu dauke da makamai don biyan dukkan bukatunsu in ban da bukatar raba kasa.

Dakarun gwamnatin kasar za su janye daga yankunan kasar biyu masu magana da yaren Turanci, kuma za ta fara tattaunawar da su dazar mayakan 'yan awaren suka aje makamansu kuma suka nuna sha'awar komawa don ci gaba da zaman rayuwar cikin al'umma, in ji shi.

Jamhuriyar Kamaru tana fama da matsanancin kalubalen tsaro a yankunan kasar biyu masu magana da yaren Turanci a shiyyar arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, inda 'yan awaren ke fafutukar kafa kasarsu mai cin gashin kanta wanda suka mata suna "Ambazonia."

A cewar MDD, sama da al'ummar kasar Kamaru 430,000 ne tashin hankali ya tilasta musu ficewa daga gidajensu, kana wasu mutane kimanin dubu 30 sun tsere zuwa makwabciyar kasar Najeriya tun bayan barkewar tashin hankalin a shekarar 2017. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China