in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya za ta kara yawan taragun jirgin kasa da Sin ta samar
2019-05-10 09:20:38 cri

Majalisar dattijan Nijeriya ta kada kuri'a tare da amincewa da kudurin kara taragu ga jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake fama da yawan matafiya a jirgin kasan mai sauri na farko da kasar Sin ta samar a yankin yammacin Afrika.

Kuri'ar da shugaban majalisar Bukola Saraki ya gudanar ta murya a jiya, biyo bayan kudurin da Ali Ndume, sanata mai wakiltar jihar Borno ya gabatar, yana mai cewa, akwai bukatar kara adadin taragun jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna domin saukaka wahalhalun fasinjojin dake bin jirgin saboda fargabar matsalar satar mutane da sauran muggan laifuffukan da ake aikatawa a kan hanyar mota.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasar, majalisar ta yi kira ga hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar, ta kara yawan zirga-zirgar jirgin, tare da daidaita farashin tikiti domin magance matsalar da ake fuskanta.

Shugaban kwamitin sufuri na majalisar Gbenga Ashafa, ya ce nan ba da dadewa ba, za a kara taragu 12 domin ba fasinjoji damar bin jirgin dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China