in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaiministan Sin ya isa Washington don tattaunawar cinikin Sin da Amurka karo na 11
2019-05-10 09:01:32 cri

Mataimakin firaiministan kasar Sin Liu He, a jiya Alhamis ya isa birnin Washington domin halartar muhimmiyar tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka karo na 11.

Liu ya fadawa 'yan jaridu jim kadan bayan isarsa cewa ya je Washington da zuciya daya, yana mai cewa, karkashin muhimmin yanayin da ake ciki a halin yanzu yana fatan zai gudanar da tattaunawa da musayar ra'ayi bisa tushen gaskiya tare da bangaren Amurka.

Liu wanda mamba ne a hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma babban jami'i mai wakiltar kasar Sin a cikakkiyar tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.

Kasar Sin ta yi amanna cewa kara kudin haraji ba shi ne zai warware matsaloli ba, in ji Liu, ya kara da cewa, matakin zai yi illa ne ga kasar Sin, da Amurka, da ma duniya baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China