in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin shawarwari ko yin cacar baki, su zama ruwan dare a lokacin da ake kokarin daidaita arangamar ciniki tsakanin Sin da Amurka
2019-05-09 17:31:15 cri

Ofishin wakilin harkokin cinikayya ta kasar Amurka a jiya Laraba ya sanar da cewa, daga gobe Jumma'a za a daga harajin da ake sanya wa kayayyakin kasar Sin da suka kai dalar Amurka biliyan 200 daga kaso 10% zuwa 25%. A game da wannan, kasar Sin ta mai da cewa, arangamar ciniki da ke ta tabarbarewa ba ta dace da moriyar al'ummar kasashen biyu da ma ta duniya ba, kuma kasar Sin ta yi bakin ciniki da matakin, idan har Amurka ta aiwatar da shi,lalle, ba yadda za a yi sai Sin ita ma ta dauki matakai.

Idan an kwatanta wadannan sanarwoyi biyu da Amurka da kuma Sin kowanensu suka bayar, za a gane cewa, na farko, Amurka ta fi jadda "shirin daukar matakin" ne, wato akwai yiwuwar ta canza ra'ayinta. Na biyu kuwa, kasar Sin ta mai da martani cikin sauri, kuma matsayinta a bayane yake.

Bangarorin biyu suka bayar da sanarwoyin ne a daidai lokacin da za a fara shawarwarin harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin manyan jami'ansu karo na 11, matakin da ya jawo hankalin al'umma, wanda kuma ya nuna mana cewa, yin shawarwari da juna a yayin da kuma suke cacar baki da juna ya riga ya zama yanayi na kullum a tsakanin kasashen biyu ta fannin daidaita arangamar cinikinsu.

Tun daga watan Faburairun bara zuwa yanzu, an samu ci gaba a shawarwarin harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, duk da haka, sau tari ne aka samu koma baya. Amma a wannan karo, ba a fara shawarwarin ba tukuna, sai Amurka ta sanar da daga harajin, to, hakan ba wani abin mamaki ba ne ga kasar Sin, kuma kasar ta Sin za ta dauki matakan da suka dace domin tinkarar abin yadda ya kamata.

A hakika dai, a yayin da kasar Amurka ke sanar da cewa, za ta kara yawan harajin kwastan kan kayayyakin cinikayyar kasar Sin, a sa'i daya kuma ta bayyana cewa, har yanzu akwai damar a gani an cimma yarjejeniya mai ma'ana kwarai a tsakanin bangarorin biyu, kana kuma ta ce, bangarorin biyu na shirin shawarwarin da za a yi tsakanin shugabannin kasashen biyu bayan cimma yarjejeniyar. Irin matakin da kasar Amurka ta dauka, ya nuna cewa, kasashen Sin da Amurka na kokarin kawar da kiki-kakar tattalin arziki da cinikayya ta hanyar yin shawarwari tare da yake-yake, hakan za su kyutata hanyar yin mu'ammala, da nufin kawar da bambance-0bambance a tsakaninsu, tare kuma da kara habaka ra'ayin bai daya.

Bisa wannan yanayin da ake ciki, za a fahimci cewa, ma ya sa a karkashin matsin lamba da kasar Amurka ta yi a fannin harajin kwastan, mambn ofishin siyasan kwamitin tsakiya na JKS, mataimakin firaministan kasar Sin, kuma mai jagoran shawarwarin tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka, Liu He ya tsaida kudurin ziyarci Amurka bisa gayyatar da aka yi masa, don halartar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya bisa babban matsayi a tsakanin kasashen biyu karo na 11 wanda za a shirya a tsakanin ranakun 9 zuwa 10 ga wata. Wannan ba domin tsoron da Sin ta yi har ta janye jiki ba, a maimakon haka, saboda tuni dai kasar Sin ta fahimci da kuma dace da irin hanyar da ake bi wajen kawar da takardamar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin bangarorin biyu, don haka ba za ta damu kan wata matsala da Amurka ta tayar ba, ta yadda za ta iya sarrafa yunkurin yin shawarwari yadda ya kamata.

Kawar da sabani ta hanyar yin shawarwari, matsayi ne da kasar Sin ke tsayawa a kai a ko da yaushe. An riga an kammala shawarwarin a tsakanin bangarorin biyu har sau 10, inda aka samu hakikanin ci gaba a fannonin sayen kayayyakin cinikayya, tsare-tsare, tsarin gudanar da aiki da dai sauransu, wannan ba cikin sauki da aka samu, akwai bukatar a kiyaye irin ci gaba. Amma, a sa'i guda akwai bukatar a warware wasu matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu. Don haka, a yayin kammala shawarwarin na zagaye na 10, bangarorin biyu suka tsaida kudurin shirya shawarwarin na zagaye na 11 a wannan mako a birnin Washington, don ci gaba da tattaunawa. Ko da yake kasar Amurka ba ta dauki matakin da ya dace ba, hakan aka tayar da matsaloli kan shawarwarin na wannan zagaye, amma hakan ba zai kawo tasiri ga kasar Sin ba. Tafi Amurka don yin shawarwari bisa shirin da aka yi, mataki ne da kasar Sin ta dauki don girmama ka'idojin shawarwarin, da kuma girmama nasarorin da bangarorin suka cimma a cikin watanni 16 da suka gabata.

Sinawa kan yi ayyuka bisa sanin ya kamata. Kasashen Sin da Amurka suna matakai daban daban a fannin bunkasar tattalin arziki, kana kuma akwai bambanci a tsakaninsu ta fuskar tsare-tsaren tattalin arziki. Kasancewar rikicin da ke tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki, ba wani abun mamaki ba ne. Kuma bullowar matsaloli a yayin tattaunawarsu ba ta wuce zaton mutane.

Yanzu Amurka ta yi shelar kara sanya haraji kan kayayyakin da take shigowa daga ketare, lamarin da ya nuna cewa, tana kara jin fushi. Ko da yake Amurka ta ce, Sin tana biyan harajin da aka kara sanyawa. Amma 'yan majalisar Amurka ba su yarda da hakan ba. James Lankford, dan majalisar dattawan Amurka kuma dan jam'iyyar Republican ya ce, yanzu 'yan kasuwan kasar wadanda suke sayen kayayyakin daga Sin sun riga sun biya wa gwamnatin Amurka harajin kwastam fiye da dalar Amurka biliyan 16. Kamfanonin Amurka ne suke biyan haraji, a maimakon 'yan kasuwan Sin masu sayar da kaya ga Amurka.

A sa'i daya kuma, kasar Sin ta san cewa, za a dauki tsawon lokaci wajen daidaita batu mai wuya da sarkakiyya na tattalin arziki da ciniki a tsakaninta da Amurka. Ba za ta sauya manufarta sakamakon wani abu ba. Tarihi ya shaida mana cewa, matsa lamba kai tsaye bai iya warware wata matsala ba. A karshe dai dole ne a koma kan teburin shawarwari. Har ila yau, ana kara samun rikici, ana kara bukatar tuntubar juna kai tsaye. Kasar Sin ta aika da tawagarta zuwa Amurka domin ci gaba da tattaunawa bisa shirin da aka tsara, a kokarin daidaita kulawar juna da kuma kara azama kan koma kan teburin shawarwari bisa sanin ya kamata.

Abu mai muhimmanci shi ne kasar Sin, wata kasa ce da ke sauke nauyinta yadda ya kamata kullum. Sau da yawa shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, huldar da ke tsakanin manyan kasashe tana da nasaba da samun kwanciyar hankali a duk duniya cikin dogon lokaci. Kasashen Sin da Amurka suna da moriyar bai daya, kuma suna sauye nauyinsu ta fuskar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da kara azama kan bunkasuwa da wadatar kasa da kasa. A shekara guda da suka wuce, rikicin da ke tsakanin kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da ciniki ya lahanta moriyarsu duka, har ma ya kawo illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Rahoton yin hangen nesa kan tattalin arzikin duniya da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya kaddamar a kwanan baya ya bayyana cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya a bana da badi zai kai kashi 3.5 cikin dari da kashi 3.6 cikin dari, wanda ya ragu da 0.2 cikin dari da kuma 0.1 cikin dari.

Lokacin da aka samu ci gaba wajen shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka kan batun tattalin arziki da ciniki, a kan samu yanayi mai kyau a kasuwannin hannayen jari na kasashen 2, gami da na daukacin duniya baki daya. Sa'an nan, lokacin da aka samu koma baya a shawarwarin, to, tabbas ne za a samu girgizar darajar hannayen jari a kasuwanni daban daban. Wannan ya nuna cewa, samun masalaha tsakanin Sin da Amurka zai haifar da alfanu ga daukacin duniya, yayin da gazawarsu wajen cimma daidaito za ta haddasa koma bayan tattalin arzikin duniya.

Ko da yake, kasar Amurka ta dauki matakin kara harajin kwastam don matsa wa kasar Sin lamba, amma duk da haka, tawagar kasar Sin ta tafi kasar Amurka don halartar shawarwari kamar yadda aka tanada a baya. Wannan batu ya nuna yadda kasar Sin take kulawa da jama'ar kasashen 2, gami da kokarin kare moriyar jama'ar sauran kasashe, da neman tabbatar da damar farfado da tattalin arzikin duniya.

Nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da shawarwari karo na 11 tsakanin Sin da Amurka dangane da batun tattalin arziki da ciniki, a birnin Washinton na kasar Amurka. Kamar yadda ta yi a baya, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta, tare da nuna cikakken sahihanci, don neman gudanar da shawarwarin yadda ake bukata. Sai dai, batun shawarwarin ya shafi bangarori 2, inda ake bukatar kasar Amurka ita ma ta nuna sahihanci, ta yadda za a samu damar kau da sabanin ra'ayi, gami da habaka hadin kai. Tuni kasar Amurka ta san manufar kasar Sin ta tushe, wato: kasar Sin ba ta son takaddamar ciniki, amma duk da haka ba ta tsoron fuskantar takaddamar. Idan ya zama wajibi, za ta shiga takaddamar da kasar Amurka ba tare da jinkiri ba. Ban da haka, kasar Sin na son daidaita sabanin ra'ayi ta hanyar hadin kai, amma sam ba za ta yarda da yadda za a lahanta babbar moriyar kasa da ta jama'arta ba.

Kome sakamakon da za a samu a shawarwarin da zai gudana cikin kwanaki 2 masu zuwa, kasar Sin za ta fuskance shi cikin natsuwa, kuma za ta ci gaba da kokarin gudanar da harkokinta, da bin turbar da ta zaba. A cikin watanni 16 da suka wuce, bangaren Amurka ya yi ta tsaurara matakan haraji kan kasar Sin, amma tattalin arzikin Sin, da al'ummar kasar, sun haye wahalar cikin nasara, har ma ana samun karin sakonni masu yakini a kasar Sin. Saboda haka, kasar Sin cike take da imani, kuma ta iya sosai, wajen tinkarar duk wani matsin lamba. Wannan kokari zai ba kasar Sin damar kyautata tsarin tattalin arzikinta, inda za ta gudanar da karin gyare-gyare a gida, da kara bude kofa ga kasashen waje, don tabbatar da cigaban kasar mai inganci, tare da baiwa duniya karin damammakin hadin gwiwa don neman ci gaban tattalin arziki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China