in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu shakka yunkurin yin amfani da batun Taiwan don harzuga kasar Sin ba zai nasara ba
2019-05-09 15:33:15 cri

A ranar 7 ga wata ne, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da shirin dokar goyon bayan yankin Taiwan na shekarar 2019, da kudurin sake tabbatar da alkawarin da Amurka ta yi wa Taiwan, da ma yadda ake martaba dokar dangantakar da ke tsakaninta da yankin Taiwan. Wannan wani lamarin siyasa ne mai hadarin gaske da Amurka ta bullo da shi domin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar amfani da batun yankin Taiwan, da nufin harzuga kasar Sin a kokarinta na samun bunkasuwa cikin lumana.

Idan har Amurka ta ci gaba da kafewa kan wannan batu, to za ta lalata hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Sin a wasu muhimman fannoni, tare da kawo cikas ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Don haka, kasar Sin ta yi Allah wadai da matakin na Amurka tare da nuna rashin jin dadinta matuka kan wannan batu.

A ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1979 ne, Sin da Amurka suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a hukumance yayin da tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ke shugabancin kasar. Bana shekaru 40 ke nan da kafuwar huldar, hakan ya sa Mr. Carter ya wallafa wani sharhi a jaridar Washington Post domin yin gargadin cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu na cikin lokaci mai sarkakiya, duk wani mataki da bai dace da zai haddasa mummunan hadari ga duniya baki daya. Don haka, dole ne 'yan siyasa a majalisar dokokin Amurka su fahimci cewa, babu shakka duk wani yunkurin yin amfani da batun Taiwan don harzuga kasar Sin ba zai yi nasara ba. Saboda akwai kurakurai uku a cikin lamarin.

Kuskure na farko shi ne, lamarin ya lalata tushen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. A matsayinsu na kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki kuma masu fada-a-ji a duniya, muddin suka kara aza harsashi mai inganci kan raya huldarsu, za a kara samun kwanciyar hankali a duniya. Tushen da aka riga aka tabbatar a cikin sanarwoyi hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka amince shi ne, kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, babban yankin kasar Sin da na yankin Taiwan na cikin kasa daya, kana jamhuriyar jama'ar kasar Sin ita ce halaltacciyar gwamnatin kasar Sin a duniya. Yadda majalisar wakilan Amuka ta ke neman kyautata dangantakar hadin kan ayyukan soja tare da yankin Taiwan, a kan yi shi ne tsakanin kasashen dake 'yanci, kuma hakan ya saba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana ya karya dokokin kasa da kasa. Idan har babu wannan tushen, to yaya za a ci gaba da raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka?

Kuskure na biyu: yi wa kasar Sin kashedi ta hanyar yin amfani da batun Taiwan, an lura cewa, a duk lokacin da huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala, sai Amurka ta rika yi wa kasar Sin kashedi ta hanyar yin amfani da batun Taiwan yayin da sassan biyu suke gudanar da shawarwari, hakika wasu 'yan siyasar Amurka sun saba da yin hakan. Duk da cewa, ya dace a yi kokarin neman samun karin moriya yayin da ake yin shawarwari, amma bai kamata ba a yi amfani da batun Taiwan yayin da ake daidaita matsala tsakanin Sin da Amurka, dalilin da ya sa haka shi ne domin batun Taiwan harkar ce ta cikin gidan kasar Sin, batun dake shafar muradun kasar Sin mai al'ummun sama da miliyan 1400, ba zai yiyu ba kasashen waje su tsoma baki a ciki, balle ma su yi amfani da batun yayin da suke yin shawarwari, a don haka kasar Sin ta sanar da cewa, idan Amurka ta yi haka, ko shakka babu ba za ta cimma burinta ba.

Kuskure na uku: idan yanayin da ake ciki game da siyasar yankin Taiwan ya gamu da tangarda, hakan zai kawo illa ga kwanciyar hankali a shiyyar. A shekarar 2018, jam'iyyar ci gaban demokuradiya ta Taiwan wadda ke makarkashiyyar samun 'yancin Taiwan ta yi rashin nasara a zaben yankin Taiwan, an yi hasashe cewa, a irin wannan yanayi, ba zai yiyu ba ta lashe zaben shugaban yankin da za a shirya a shekara mai zuwa. Amurka ta sake nuna goyon bayanta ga masu neman samun 'yancin Taiwan. To, ana ganin cewa, ya kamata wasu 'yan siyasar Amurka su sake karanta sharhin da Jimmy Carter ya wallafa a jaridar Washington Post, ta haka za su fahimta cewa, idan ba za a iya daidaita batun Taiwan yadda ya kamata ba, hakan zai kawo tashin hankali a shiyyar, tare da tayar da hargitsi a daukacin kasashen duniya baki daya, kuma da gaske lamarin zai faru, ba tsorata jama'a ake yi ba kawai.

A watan Afrilun bana, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bugawa Jimmy Carter waya, inda ya nemi shawarar tsohon shugaban kasar kan yadda za a yi mu'amala da kasar Sin. Rahotanni na cewa, daya daga shawarar da Jimmy Carter ya bayar ita ce, "Bai kamata a tayar da yaki ba". Idan 'yan siyasar kasar Amurka suna son lalata ka'ida mafi muhimmanci da kasar Sin take bi kan batun Taiwan, alal misali, idan sojojin jiragen teku na kasar Amurka suka isa yankin Taiwan, tabbas zai zama lokacin da kasar Sin za ta soma neman dinkewa da yankin Taiwan.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sha nanata cewa, kasar Sin na kokarin daidaita huldar tsakaninta da manyan kasashe da yin hadin gwiwa tsakaninsu, tana kuma fatan zaman tare da sauran manyan kasashe cikin lumana. Bugu da kari, kasar Sin, tana fatan za su girmama juna da yin hadin gwiwa domin neman nasara tare maimakon tayar da rikici da takaddama tsakaninsu. Ya kamata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, wato daya daga cikin huldodi mafiya muhimmanci tsakanin kasashen biyu a duniya, ta neman ci gaba ba tare da tangarda ba bisa ka'idojin samun daidaito da hadin gwiwa tsakaninsu, bai kamata a canja wannan ka'ida ba. Haka kuma bai dace wasu 'yan siyasar kasar Amurka su yiwa aniyyar al'ummar Sinawa bahuguwar fahimta kan batun yankin Taiwan.(Kande, Jamila, Sanuni)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China