in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin sana'o'i na kasar Amurka sun ki amincewa da manufar karbar karin harajin kwastam
2019-05-09 14:50:02 cri
Gwamnatin kasar Amurka ta sanar a kwanakin baya cewa, za ta kara yawan harajin kwastam da take karba kan kayayyaki kirar kasar Sin da ake shigarwa Amurka da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200 , daga kaso 10% zuwa 25%. Dangane da wannan batun, hadaddiyyar kungiyar 'yan kiri ta kasar Amurka, da kungiyar masu sana'ar sadarwa ta kasar, gami da sauran kungiyoyin sana'o'i daban daban fiye da 10 na kasar, dukkansu sun sanar da kin amincewa da wannan mataki. A ganinsu, a karshe jama'ar kasar Amurka ne za su yi hasara. Saboda haka, suna bukatar gwamnatin Amurka da ta kara yin mu'amala da kasar Sin, ta yadda za su cimma matsaya tsakaninsu ba tare da bata lokaci ba.

A nasa bangare, Davis French, mataimakin shugaban kungiyar 'yan kiri ta kasar Amurka, ya sanar a ranar 5 ga watan da muke ciki cewa, yadda Amurka ta dauki wannan mataki na sanya karin haraji ba zato ba tsammani zai haifar da babbar matsala ga harkokin kamfanonin kasar Amurka, musamman ma kanana da matsakaitan kamfanoni, tare da haddasa raguwar guraben ayyukan yi, gami da matsalar hauhawar farashin kaya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China