A jiya ne kasashen dake yankin kahon Afirka, suka yi alkawarin ba da goyon baya don takaita kaurar jama'a, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaban da ake bukata.
Darektan sashen lafiya da ci gaban walwalar jama'a a hukumar raya kasashen gabashin Afirka (IGAD), shi ne ya bayyana hakan a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin da yake jawabi a bikin bude taron kasa da kasa kan yadda ake tilastawa jama'a barin matsugunansu. Yana mai cewa, daidaita wannan matsala, za ta yi kyakkyawan tasiri ga tattalin arziki da yanayin zaman takewar jama'a.
A don haka, ya bukaci da a bullo da managartan manufofi da dokoki, domin kare da kuma baiwa al'ummomin dake fadawa cikin wannan matsala 'yanci tare kuma da kara gina al'ummomin da wannan matsala ta shafa.(Ibrahim)