in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bullo da sabbin matakan kara bude kofa ga ketare
2019-05-09 09:38:01 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana kudurin kasarsa na hanzarta bunkasa harkokin kirkire-kirkire cikin shirinta na yankunan raya tattalin arziki da fasahar kere-kere na kasa, a wani mataki na kara bunkasa tattalin arziki mai inganci da bullo da wasu matakai na zurfafa gyare-gyare da bude kofa.

An yanke wannan shawara ce yayin zaman majalisar zartarwar kasar da firaminista Li Keqiang ya jagoranta. Yana mai cewa, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan shirin raya kirkire-kirkire na yankunan raya tattalin arziki da fasahar kere-kere na kasa. A don haka, ya ce, akwai bukatar a ci gajiyar yankunan raya tattalin arziki da fasahar kere-kere na gwajin yadda ya kamata a fannin zuba jarin waje, kana a ci gaba da tsara manufofi da dokoki ta yadda wadannan cibiyoyin za su janyo hankulan masu sha'awar zuba jari daga ketare.

A shekarun 1980 ne dai, kasar Sin ta yanke shawarar kirkiro wadannan yankuna, a wani bangare na matakan da take dauka na kara bude kofarta ga ketare. A shekarar 1984 kuma aka bude yanki na farko, yanzu haka akwai irin wadannan yankuna guda 219, inda suke mayar da hankali kan manyan hidimomin kerawa da samar da kayayyaki, matakin da zai kai ga shirin kasar Sin na raya birane zuwa ga alakar kasa da kasa da raya masana'antu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China