in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Namibia ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin SADC da ECOWAS
2019-05-09 09:26:18 cri
Shugaban kasar Namibian kana shugaban gudanarwar kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika (SADC), Hage Geingob, ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen Namibia da Guinea zai iya kara dankon zumunta tsakanin kungiyar SADC da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato (ECOWAS).

Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai lokacin ziyarar aiki da shugaban kasar Guinea, Alpha Conde, ya kai zuwa Windhoek, babban birnin kasar Namibia.

"Wannan irin hadin gwiwar yana da muhimmanci a kokarin da muke na tabbatar da cimma nasarar ajandar nan ta raya ci gaba nan da shekarar 2063 da kuma daga matsayin nahiyar Afrika wanda dukkanninmu muke da burinsa. Muna bukatar samar da guraben ayyukan yi, musamman ga matasa. Wannan shi ne babban abin da muka sanya a gabanmu, ya kamata dukkanmu mu yi aiki tukuru wajen samar da ingantaccen muhallin kasuwanci, da daga matsayin zuba jari, da tallafawa bunkasuwar kanana da matsakaitan sana'o'i (SMEs)."

Ya ce, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zai kasance a matsayin wata dama ce ta habaka shigi da ficin cinikayyar kayayyakin bukatun yau da kullum tsakanin kasashen Afrika. A cewar Geingob, wannan mataki zai bada gudunmmawa wajen tabbatar da tsarin nan na ciniki maras shige a tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika.

Conde ya kai ziyarar aikin kwanaki biyu ne zuwa Namibia wanda zai karkare ziyararsa a yau Alhamis. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China