in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka zai lahanta tsarin zuba jarin kasa da kasa: Juncker
2019-05-08 10:39:11 cri
Batun takaddamar cinikayya tsakanin kasar Sin da Amurka zai iya haifar da mummunar illa game da tsarin zuba jarin kasa da kasa muddin ba'a dauki kwararan matakan warware matsalar cikin hanzari ba, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai wato (EC), Jean-Claude Juncker shi ne ya bayyana hakan.

"Dangane da batun alakar ciniki tsakanin Sin da Amurka, ina ganin cewa, babbar matsalar dake shafar matsalolin tattalin arzikin da duniya ke fuskanta ya ta'allaka ne da batun takaddamar cinikin da ta kaure tsakanin Amurka da Sin," Juncker ya bayyana hakan ne a taron manema labarai.

"Idan har masu zuba jari ba su jin cewa wannan matsalar za'a iya warware ta cikin kankanin lokaci, karsashin zuba jari a dukkan bangarorin yankin Atlantika da sauran sassan duniya zai iya samun koma baya," in ji shi.

Ko a ranar Talata ma, sai da kasar Sin ta nanata aniyarta na ci gaba da tattaunawar warware sabanin ciniki tsakaninta da Amurka da zuciya daya, Sin ta nuna cewa ba ta da wani mummunan kudurin neman ruruta wutar rikicin kasuwanci tsakaninta da takwararta, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ayyana. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China