in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta haramta amfani da Babura a jihar Adamawa
2019-05-08 09:56:17 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar 'yan sandan kasar, ta haramta amfani da Babura a jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da tashin hankali, adadin jihohi 8 ke nan da aka haramta hawan Babura a kasar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa Othman Abubakar shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe. Ya ce, an dauki wannan mataki ne, domin daidaita yadda bata gari ke amfani da Babura barkatai suna aikata munanan laifuffuka kamar satar mutane, da fashi da makami da fadan kabilanci gami da sauran munanan laifuffuka a jihar.

Don haka, rundunar za ta fara gudanar da wani sintiri na musamman, za kuma ta kama duk wanda aka samu yana karya wannan umarni. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China