in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
BRI za ta samar da karin damarmaki ga kasashe masu tasowa
2019-05-08 09:34:57 cri
Mukaddashin karamin jakadan karamin ofishin jakadancin kasar Sin a Lagos na Nijeriya, Guan Zhongqi, ya ce taro na 2 na hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da aka kammala kimanin mako guda da ya gabata, zai kara karfafa ci gaban kasa da kasa da samar da karin damarmaki ga kasashe masu tasowa, ciki har da Nijeriya.

Guan Zhongqi, ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a jiya dangane da sakamakon taron BRI na 2, inda ya ce Nijeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, da muhimmiyar rawar da za ta taka a cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Shawarar wadda kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013, manufa ce mai dogon zango da ta shafi nahiyoyi da shirye-shiryen zuba jari da nufin raya ababen more rayuwa da gaggauta dunkulewar tattalin arzikin kasashen da dadaddiyar hanyar cinikayyar Siliki ta ratsa.

Ya kara da cewa, shawarar ta samar da sabbin damarmaki ga Nijeriya da Sin, wadanda za su tabbatar da dorewar dangantakarsu, yana mai cewa taron da aka yi a Beijing, na kunshe da dimbin abubuwan da za su amfanawa kasashen 2. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China