in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia ta ayyana dokar ta baci kan fari
2019-05-07 09:52:54 cri

Gwamnatin Namibia, ta ayyana dokar ta baci a kasar ta kudancin Afrika da fari ya aukawa.

Shugaban kasar Hage Geingob, ya ce ayyana dokar ta biyo bayan tuntubar majalisar zartarwar kasar da sauran sassan gwamnati, karkashin tanadi na 26 na kundin tsarin mulkin kasar.

Ya ce, lokacin damina na gab da karewa, kuma ba a samu isasshen ruwan sama ba. Yana mai cewa, wannan na nufin za a fuskanci iftila'in fari wanda kuma zai shafi mutane da dama a kasar.

Shugaba Geinob ya ce, ofisoshi da ma'aikatu da hukumomin da sauran masu ruwa da tsaki za su yi aiki tare, domin tabbatar da an kai taimakon da ya dace ga al'ummomin da lamarin ya shafa.

A cikin wannan yanayi, gwamnati za ta yi kokarin kare al'ummar kasar da dabbobinsu daga fari a ko da yaushe.

Tun shekarar 2013, Namibia ke jurewa farin dake ta auka mata, lamarin da ya yi mummunan tasiri kan galibin sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China