in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya tattauna da takwaransa na Eritrea
2019-05-07 09:19:26 cri

A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna da takwaransa na kasar Eritrea Osman Saleh a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin ganawar tasu, Wang Yi ya bayyana cewa, kasarsa tana martaba dadaddiyar alakar abota dake tsakanin kasashen biyu, kuma bangaren kasar Sin na fatan karfafa musaya, da fahimtar juna, da zurfafa amincewa da juna gami da samun ci gaba tare da bangaren Eritrea.

Ya ce, Sin na gudanar da alaka da kasashen Afirka ne bisa tushen rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna. Kuma kasarsa a shirye take ta yi aiki da kasashen Afirka, ciki har da kasar Eritrea wajen kare 'yanci da muradun kasashe masu tasowa.

A nasa jawabi, Osman Saleh ya ce, kasarsa tana daukar kasar Sin a matsayin dadaddiyar abokiya ta kwarai. Bangaren Eritrea yana maraba da kasar Sin da ya taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kahon Afirka, kana a shirye kasarsa ta ke ta bunkasa musaya da hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China