in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin: Tawagar kasar Sin na shirin zuwa Amurka don yin shawarwari
2019-05-06 19:20:45 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin a nan birnin Beijing cewa, Sin na fatan Amurka za ta ba da hadin gwiwa, ta yadda bangarorin biyu za su cimma yarjejeniyar samun moriyar juna bisa tushen girmama juna. Ya kara da cewa, tawagar kasar Sin na shirin zuwa Amurka don yin shawarwari.

A jiya Lahadi, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, daga ranar 10 ga wata, Amurka din za ta kara harajin da take sanyawa kayayyakin da suka kai dalar Amurka biliyan 200 da take shigowa daga kasar Sin daga kaso 10% zuwa 25%.

A game da wannan furuci, Geng Shuang ya ce, "hakan ya faru ne sau da dama, kuma matsayin kasar Sin a bayane ne yake. Kawo yanzu an gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya har sau 10 a tsakanin Sin da Amurka tare da samun ci gaba. Abin da aka sanya a gaba shi ne kasashen biyu su hada kansu, a kokarin cimma yarjejeniyar samun moriyar juna, kuma hakan ba wai kawai ya dace da moriyar kasar Sin ba ne, har ma da ita kan ta Amurka." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China