in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sanar da shirinta na murnar ranar wurin adana kayayyakin tarihin kasa da kasa
2019-05-06 11:11:57 cri

Hukumar dake kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin (NCHA) ta sanar a jiya Lahadi cewa, za'a gudanar da bikin tunawa da ranar cibiyoyin adana kayayyakin tarihi ta kasa da kasa wanda ya dace da ranar 18 ga watan Mayu.

Cibiyar adana kayayyakin tarihi ta lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin ita ce za ta dauki bakuncin shirya wani gagarumin bikin baje kolin musamman game da ruhin wayewar kan al'ummar Sinawa.

Sauran cibiyoyin adana kayayyakinn tarihi a fadin kasar Sin su ma za su kaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka shafi jigon bikin mai taken "Gidan adana kayayyakin tarihi a matsayin cibiyoyin raya al'adun gargajiya: makomar al'adun gargajiya," in ji hukumar ta NCHA.

Guan Qiang, mataimakin daraktan hukumar ya ce, shagulgulan za su mayar da hankali ne kan batun muhimmanci da irin rawar da cibiyoyin adana kayayyaki ke takawa wajen kiyaye al'adun da aka gada tun zamanin kakanni, kuma ana sa ran cibiyoyin za su mayar da hankali wajen daga matsayin sauye sauye da raya ci gaban fasahohin kirkire kirkire ta hanyar kyawawan al'adun gargajiyar kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China