in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 41 sun mutu a hadarin jirgin saman da ya kama da wuta a Moscow
2019-05-06 11:09:40 cri

A yau Litinin kwamitin binciken kasar Rasha ya tabbatar da mutuwar mutane 41 bayan da wani jirgin saman fasinja samfurin SSJ-100 wanda ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Murmansk na arewa maso yammacin kasar Rasha ya kama da wuta bayan da ya yi saukar gaggawa a ranar Lahadi a filin jirgin saman kasa da kasa na Sheremetyevo a birnin Moscow.

Mutane 37 sun tsira a hadarin jirgin saman mai dauke da mutane 78 a sanarwar farko da kwamitin ya fitar.

Rahotanni na cewa, jirgin saman ya tashi ne daga filin jirgin saman Sheremetyevo da misalin karfe 18:00 agogon kasar daidai da karfe (1500 agogon GMT), daga bisani ya yi saukar gaggawa bayan da ya dinga shawagi a yankunan birnin Moscow mintoci 40 bayan tashinsa.

Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ruwaito cewa, jirgin ya kama da wuta ne tun gabanin ya yi saukar gaggawa.

Da farko an ba da rahoton cewa, tsawa ce ta haifar da tashin gobarar jirgin saman.

Kwamitin ya fara yin bincike game da take dokokin kiyaye haddura da kamfanonin jiragen sama ke yi tare kuma da fara bincike kan musabbabin hadarin jirgin saman, in ji sanarwar.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China