in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 15 za su halarci bikin baje kolin yawon shakatawa na Tanzaniya
2019-05-06 10:09:39 cri

Rahotanni daga kasar Tanzaniya na cewa, a kalla kasashe 15 daga sassan duniya ne ake sa ran za su halarci bikin baje kolin yawon shakatawa na duniya na Karibu Kili, da zai gudana a birnin Arusa daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Yunin wannan shekara.

Da yake karin haske, jami'in tsare-tsaren bikin Dominic Shoo, ya bayyana cewa, halartar kasashen ketare cikin wannan biki, zai taimaka wajen yayata dimbin wuraren bude ido da Allah ya horewa kasar dake gabashin Afirka.

Jami'in ya shaidawa taron manema labarai cewa, masu baje kolin kayayyakin yawon bude ido na cikin gida sama da 400 za su hadu da takwarorinsu daga sauran kasashe 15 da za su halarci bikin.

A nasa jawabin, jami'in kasuwanci dake aiki a wuraren yawon shakatawa na kasar Victor Kitansi, ya ce, hukumar kare namun daji ta kasar, za ta ci gaba da taimakawa bikin yawon bude ido domin amfanin kasar.

Alkaluman hukuma na nuna cewa, bangaren yawon bude ido, shi ke kan gaba wajen samarwa kasar Tanzaniya kudaden musayar ketare, inda ya ke ba da matsakaicin gudummawar dalar Amurka biliyan biyu a shekara, daidai da kaso 25 cikin 100 na daukacin kudaden musayar da kasar take samu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China