in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sanar da ka'idojin raya birane da yankunan karkarar kasar
2019-05-06 09:13:20 cri

A jiya ne kwamitin koli na JKS da majalisar gudanarwar kasar suka sanar da hadaddun ka'idojin raya birane da yankunan karkarar kasar.

Manufar wadannan ka'idoji dai, ita ce kawar da duk wasu shingaye dake hana ruwa guda game da farfado da yankunan karkara da hanzarta zamanantar da aikin gona da raya yankunan karkara. Bisa ga tsarin, za a fara aiwatar da shirin raya birane da yankunan karkarar kasar ce nan da shekarar 2022. Haka kuma, sannu a hankali kasar Sin za ta kawar da abubuwan dake kawo tarnaki ga gidajen kwana na birane.

Kasar Sin dai na fatan bullo da managartan matakai, da za su kai ga raya birane da yankunan karkarar kasar nan da shekarar 2035. Za kuma a rage gibin dake akwai a fannin ci gaba da ma yanayin zaman rayuwa tsakanin birane da yankunan karkara.

Ya zuwa tsakan wannan karni, kasar Sin na fatan cimma nasarar manufar raya birane da kauyuka da farfado da yankunan karkara da ma cimma nasarar manufar samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adam.

Tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen zamanantar da birane da daidaita ci gaba tsakanin birane da yankunan karkarar kasar. Ko da yake, har yanzu ana fuskantar wasu matsaloli dangane da ci gaban birane da yankunan karkarar kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China