in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin mai cike da kuzari
2019-05-05 20:54:03 cri
Hutun ranar ma'aikata ta wannan shekara da ya kare ba da jimawa ba yana da dan bambanci ga Sinawa, a saboda yadda ya bunkasa harkokin cinikayya a nan kasar. A wannan shekara, gwamnatin kasar Sin ta amsa kirar al'umma kuma ta daidaita hutun ranar ma'aikata wadda ta fado a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara daga kwanaki uku zuwa hudu, karon farko da aka tsawaita hutun a cikin shekaru 10 da suka wuce. Kididdigar da ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa ta kasar ta fitar ta nuna cewa, a cikin kwanakin hudu da suka wuce, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci sassan shan iska na kasar ya kai har miliyan 195, wadanda kuma suka kashe kudin da ya kai yuan biliyan 117.67, adadan da ya karu da kaso 13.7% da ma kaso 16.1% bisa na makamancin lokacin bara.

Hakan kuma ya faru ne a sakamakon yadda tattalin arzikin kasar Sin ke gudana yadda ya kamata a cikin shekarar 2019. A farkon watanni uku na wannan shekara, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kaso 6.4%, wanda ya kasance tamkar wani babban inji na bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Haka kuma a cikin watannin ukun, yawan kudin da al'ummar suka kashe wajen sayayya sun samar da babbar gudummawar da ta kai kaso 65.1% ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, kuma hakan ya zama babban abin da ke taimakawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Wani muhimmin aiki dake gaban gwamnatin kasar Sin a wannan shekara, shi ne inganta sayen kayayyaki yadda ya kamata, an jaddada cewa, "Ya kamata gwamnatin kasar ta dauki matakan da suka dace, don inganta karuwar kudin shiga na mazauna birane da kauyuka, hakan zai karfafa karfinsu na sayen kayayyaki". Wadannan matakan sun hada da aiwatar da shirin rage harajin da za a biya na jimilar RMB yuan kimanin miliyan 200, don sanya mutane miliyan 80 su ci gajiyar shirin rage haraji, kana da "dacewa da sabon sauyin bukata da ke akwai kan sayen kayayyaki, da kara samar da kayayyaki da hidima masu inganci ta hanyoyi daban daban", "raya yawon shakatawa a shiyya-shiyya, da habaka sana'ar yawon shakatawa" da dai sauransu.

Inganta sayen kayayyaki yadda ya kamata ta hanyar raya sana'ar yawon shakatawa iri daban daban, wani mataki ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka don biyan sabbin bukatun jama'ar dake kokarin samun ingancin zaman rayuwa, da tabbatar da samun ci gaba mai inganci. Yanzu an soma ganin amfaninsa. Wani binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kusan kashi 40 cikin 100 na Sinawa sun bayyana cewa, suna son kara kashe kudi a bangaren yawon shakatawa.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin na kasa da kasa na farko da aka gudanar a bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, "Sakamakon yanayin karuwar sayen kayayyaki da kasar ke ciki, kasar Sin za ta dauki matakan inganta kudin shiga da mazauna ke samu, da kara karfinsu na sayen kayayyaki, da kara raya boyayyen karfi na kasuwar cikin gida, da kara habaka shigo da kayayyaki." A lokacin hutun ma'aikata na bana, Sinawa sun kara nunawa duniya kasar Sin mai kuzari, kana da bayyana imaninsu da fatansu kan zaman rayuwarsu da ma ci gaban kasarsu a nan gaba.(Masu fassara:Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Dukkansu ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China