in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu na inganta yanayinta don saukaka kai ziyara kasar
2019-05-04 16:51:53 cri
Afrika ta kudu ta inganta yanayinta domin saukakawa masu yawon bude ido ziyartar kasar da kuma ci gaba da kyautata yanayin don jan hankalin karin mutane.

Ministan kula da harkokin bude ido na kasar Derek Hanekom, ya bayyanawa manema labarai jiya a Durban cewa, nan ba da dadewa ba kasar za ta fara bayar da visa ta intanet.

Ya ce kasar na son bada damar shiga kai tsaye ba tare da visa ba, kana suna son gaggauta fara bayar da visar ta kafar intanet. Har ila yau, ya ce shugaban kasar na da muradin mutane su rika shiga kasar ba tare da wani tarnaki ba, da nufin inganta bangaren na yawon bude ido.

Darakta Janar na sashen yawon bude ido na ma'aikatar, Victor Tharage, ya ce an riga an tsara yadda za a rika bayar da visar ta intanet, inda a yanzu ake matakin gwaji, kafin daga bisani a kaddamar nan ba da jimawa ba.

Minsitan ya ce suna son saukaka abubuwan da ake bukata daga masu ziyartar kasar daga kasashen Sin da Indiya da Najeriya, domin za su iya bunkasa bangaren. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China