in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Japan sun yi gamgamin nuna adawa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska
2019-05-04 16:44:50 cri
A jiya Juma'a 3 ga watan Mayu, ake cika shekaru 72 da fara amfani da kundin tsarin mulkin kasar Japan na yanzu.

A kuma jiyan ne, jam'iyyar LDP mai mulkin kasar, ta sanar da aniyarta ta kara azama kan tattaunawa da al'ummar kasar dangane da yi wa kundin tsarin mulkin gyaran fuska tare da kokarin tabbatar da cimma daidaito cikin majalisar dokokin kasar game da batun.

A sa'i daya, dubban al'ummar kasar ne suka yi gangami a birnin Tokyo, hedkwatar kasar, domin tunawa da cika shekaru 72 da fara aiwatar da kundin tsarin mulkin kasar na yanzu, inda kuma suka yi kira da a yi tsayuwar daka wajen kiyaye tanadi na 9 dake kunshe cikin kundin tsarin mulkin.

Jam'iyyu da dama da ba sa mulkin kasar, su ma sun ki amincewa da kalaman jam'iyyar LDP.

An fara aiwatar da kundin tsarin mulkin kasar Japan na yanzu ne daga ranar 3 ga watan Mayun shekarar 1947. Tanadi na 9 dake cikin kundin tsarin mulkin kasar ya ce, Japan ta dakatar da tayar da yaki da yin barazanar amfani da karfin soja ko kuma daidaita rikicin kasa da kasa ta hanyar amfani da karfin soja har abada. Bisa cimma wannan manufa, Japan ba za ta kafa rundunar soji ba, kuma ba za ta yi yaki ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China