in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin ministan harkokin wajen Syria ya ce, gwamnatin kasar za ta kiyaye hadin kan kasa
2019-05-03 16:08:27 cri

A jiya ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mekdad, ya ce gwamnatin kasarsa za ta kiyaye hadin kan kasa, za ta kuma maido da dukkan yankunan kasar karkashin shugabancinta.

A lokacin da yake zantawa da manema labaru a wannan rana, Mekdad ya ce, gwamnatin kasar tana aiwatar da manufar kiyaye hadin kan kasa kan dukkan 'yan kasar Syria. Gwamnatin tana kuma kokarin 'yantar da yankin Idlib, da yankunan arewacin kasar, da na arewa maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa, tilas ne dakarun Kurdawa na Syria, su nuna biyayya ga kasarsu, a maimakon abokan gaba na kasar. Kaza lika tilas ne su nuna biyayya ga aniyar dinkewar yankunan kasar da hadin kan jama'ar ta. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China