in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin: an bayyana sakamakon zaben majalisar dokokin kasar
2019-05-02 16:25:29 cri

A daren ranar 30 ga watan Afrilun ne, hukumar harkokin zaben kasar Benin mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaben majalisar dokokin kasar, inda jam'iyyar kawancen ci gaba ta kasar ta lashe yawancin kujerun majalisar jama'ar kasar, yayin da jam'iyyar kawancen jamhuriya ta kasar ta lashe sauran kujeru.

A ranar 28 ga watan Afrilun bana ne, aka fara jefa kuri'ar zaben 'yan majalisar jama'ar Benin, inda jam'iyyar kawancen ci gaba ta kasar da jam'iyyar kawancen jamhuriya ta kasar suka fafata domin lashe kujerun majalisar guda 83. Wasu jam'iyyun da suke goyon bayan shugaban kasar na yanzu Patrice Talon sun hade, inda suka kafa wadannan jam'iyyu 2 da aka ambata a baya.

A cikin dukkan cibiyoyin jefa kuri'a guda 546 da ke fadin kasar Benin, wasu 39 ba su bude ba sakamakon barkewar hargitsi.

Bayanai na cewa, dukkan jam'iyyun 'yan hamayya na Benin ba su shiga zaben ba saboda ba su cika ka'idojin da kundin ka'idojin tafiyar da jam'iyyu da aka kafa a bara ya tanada ba. Kafin zaben, wasu jam'iyyun 'yan hamayya sun ba da sanarwar hadewa, inda suka yi kira da a kaucewa zaben na wannan karo. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China